Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar NNPP, Bayanai Sun Fito

Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar NNPP, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da jam’iyyu da dama suka fitar da ‘yan takarar gwamna a zaben jihar Edo, jam’iyyar NNPP ta sanar da nata dan takarar
  • Jam’iyyar ta sanar da fitaccen Fasto, Dakta Azehme Azena a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo – Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jam’iyyu da dama sun fitar da ‘yan takara a zaben.

Jam’iyyar NNPP ta fitar da sunan fitaccen Fasto, Dakta Azehme Azena a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Ganduje ya fadi babban dalilin da zai sa su yi wa PDP dukan alatsine a zabe, ya bugi kirji

Malamin addini ya lashe zaben fidda gwani a jam'iyyar NNPP
Fasto Azena ya zama dan takarar gwamna a jam'iyyar NNPP a zaben jihar Edo. Hoto: Dr. Azemhe Azena.
Asali: Facebook

Yanayin da jama'a suka shiga na murna

Jama’a da dama sun shiga yanayin farin ciki bayan nasarar Fasto Azena saboda su na da tabbacin jihar za ta tsira a hannunsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan nasara ta Azena ta karawa magoya bayansa karfin gwiwar samun sauki a jihar ganin yadda ta shiga wani yanayi, cewar Leadership.

Magoya bayan nasa su na da tabbacin samun sauyi a jihar inda suka ce tabbas Azena shi ne kadai zai cire a kangin da jihar ta ke ciki, cewar Vanguard.

Sauran 'yan takarar jam'iyyu a zaben

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekara.

Jam’iyyar APC a bangarenta, ta sanar da sunan Sanata Monday Okpebholo a matsayin dan takararta.

Yayin da a jam’iyyar PDP, mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu ya sha kaye bayan Asue Ighodalo ya kasance wanda zai yi takara a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Obaseki Vs Shaibu: Mataimakin gwamnan Edo ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a PDP

Har ila yau, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta NBA, Olumide Akpata ya yi nasarar zama dan takarar jam’iyyar LP.

NNPP ta roki ‘yan Najeriya kan Tinubu

Kun ji cewa uban jam’iyyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam ya roki ‘yan Najeriya karin hakuri kan halin da ake ciki.

Boniface ya ce a yanzu Shugaba Tinubu ya na bukatar goyon baya ne da kuma addu’o’i don samun nasarar dakile matsalolin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel