Edo: Murna Yayin da Deleget Ta Haihu a Wurin Zabe, Ta Raɗa Wa Jaririn Suna Mai Ban Mamaki

Edo: Murna Yayin da Deleget Ta Haihu a Wurin Zabe, Ta Raɗa Wa Jaririn Suna Mai Ban Mamaki

  • Zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Edo ya zo da abun murna da farin ciki yayin da wata Deleget mace ta haifi zankaɗeɗen jariri namiji
  • An ce matar ta fara naƙuda ne a wani Otal da aka aje su, ita da sauran deleget, inda mutanen da ke wurin suka taimaka mata har ta haihu
  • Ƙarin abun farin cikin da ya bai wa kowa mamaki shi ne ta raɗawa jaririn suna Asue Ighodalo, ɗan takarar da suke so wanda ya lashe zaɓen daga baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024 ta zama ranar farin ciki da murna a jam'iyyar PDP reshen jihar Edo a wurin zaɓen fidda ɗan takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Farashin dala zai faɗi warwas a Najeriya nan ba da daɗewa ba, gwamna ya magantu

Hakan ta faru ne sakamakon ɗaya daga cikin deleget ta haihu a wurin zaben fidda gwanin PDP kuma rahotanni sun nuna ta sauka lafiya, ta haifi ɗa namiji.

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.
Murna Yayin da Seleget Ta Haihu a Wurin Zaben Fidda Gwanin PDP a Jihar Edo Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Twitter

An tattaro cewa deleget ɗin ta fara naƙuda ne a wani Otal da aka kai su wanda ba a bayyana sunansa ba a Benin, ita da sauran deleget masu kaɗa kuri'a a zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taya matar ta haihu a wurin zaben fidda gwanin PDP?

PM News ta tattaro cewa matar mai juna biyu kuma deleget da ba a faɗi sunanta ba ta fito ne daga yankin ƙaramar hukumar Igueben a jihar Edo.

Sauran deleget ɗin da ke kewaye da ita ba su yi wata-wata ba suka taimaka mata har Allah ya sauke ta, ta haifi zankaɗeɗen jariri namiji.

Bayan haka ne matar wacce ke cike da farin ciki ta raɗa wa yaron suna Asue, sunan ɗan takarar da suke goyon baya a zaben fidda gwanin, Asue Ighodalo.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Gwamnan APC ya tausaya wa talakawa, ya ɗauki muhimman matakan da za a samu sauƙi

Wasu bayanai sun nuna cewa Ighodalo da mai ɗakinsa sun ziyarci matar da jaririn da ta haifa yayin da suka taya ta murna da farin ciki.

Waye ɗan takarar gwamnan PDP a Edo?

Rahoto ya zo daga baya cewa Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben fidda ɗan takarar gwamnan jihar Edo wanda aka yi ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024.

Attajirin ɗan kasuwa kuma lauya, Asue Ighodalo, shi ne ya samu nasarar doke ƴan takara 9 ciki harda mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel