Wata Sabuwa: Mataimakin Gwamnan PDP Ya Bankado Wata Sabuwar Makarkashiya da Aka Shirya Masa

Wata Sabuwa: Mataimakin Gwamnan PDP Ya Bankado Wata Sabuwar Makarkashiya da Aka Shirya Masa

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya koka kan sabon shirin tsige shi da ake yi daga muƙaminsa
  • Shaibu ya yi nuni da cewa sabon shirin tsige shi daga kan muƙamin nasa ya biyo dagewarsa cewa shine ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar PDP
  • Sai dai, Shaibu ya yi nuni da cewa hakan ba zai sanya ya tsorata ba ya fasa ƙoƙarin gwanin ya ƙwaci haƙƙinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya koka kan sabon shirin tsige shi daga kan muƙaminsa.

Hakan ya biyon zamansa a matsayin ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen fidda gwanin gwamnan da ɓangarensa ya gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala yayin da dan takarar gwamna ya yi barazanar daukar mataki 1 a kanta

Shaibu ya bankado sabuwar makarkashiya
Shaibu ya koka kan sabon shirin tsige shi Hoto: Philip Shaibu
Asali: Facebook

Shaibu wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ƴan jarida daga jihar Edo a Abuja jiya, ya ce tawagarsa ce ta bayyana ma sa yunƙurin tsige shi, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaibu, wanda yayi takun-saƙa da ubangidansa, Gwamna Godwin Obaseki, ya sha alwashin ci gaba da shirye-shiryensa ko da yin hakan zai sa majalisar dokokin jihar ta tsige shi, rahoton The Punch ya tabbatar.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne jami’in zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana Asue Ighodalo a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin, inda ya samu ƙuri’u 577.

Me Shaibu ya ce kan shirin tsige shi?

Sai dai, Shaibu ya bayyana kansa a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan, inda ya bayyana zaɓen fidda gwanin da ya haifar da Ighodalo, wanda Gwamna Obaseki ke marawa baya, a matsayin ba komai ba face taron biki.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

A kalamansa:

"Ko yanzu da muke magana, an yi ta kirana cewa, ‘dubi abin da waɗannan mutanen suke yi. Suna cewa za su tsige ka, cewa ka yi nisa baka jin kira.’ Suna barazanar tsige ni.
"Ni kuma na ce idan fafutukar ƙwato ƴancina kamar yadda yake a kundin tsarin mulki shi ne zai jawo tsige ni, ba matsala, saboda ƙwato ƴancina haƙƙi ne da nake da shi a kundin tsarin mulki kuma ba wanda ya isa ya ƙwace shi.
"Don haka idan haƙƙina da yake a cikin kundin tsarin mulki shi ne zai sanya su tsige ni, akwai kotu, za su yi abin da ya dace."

Idahosa Ya Yi Zanga-Zanga a Hedikwatar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a zaɓen fidda gwani na jihar Edo, Dennis Idahosa, ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen fidda gwanin.

Dennis da magoya bayansa sun dira a hedikwatar jam'iyyar APC ta ƙasa inda suka buƙaci kwamitin NWC da ya abin da ya dace don tabbatar da adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel