APC Ta Shiga Matsala Bayan Dan Takarar Gwamna Ya Yi Barazanar Daukar Wani Mataki 1 a Kanta

APC Ta Shiga Matsala Bayan Dan Takarar Gwamna Ya Yi Barazanar Daukar Wani Mataki 1 a Kanta

  • An ƙara samun dirama yayin da ake ta cece-kuce kan zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Edo
  • Ɗaya daga cikin masu neman takarar Hon. Dennis Idahosa, ya nuna rashin jin daɗinsa game da sakamakon zaɓen kuma ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a
  • Hon. Idahosa da magoya bayansa sun yi dafifi a gaban hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja domin ƙalubalantar zaɓen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani ɗan takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar kwanan nan a jihar Edo, Hon. Dennis Idahosa, ya jagoranci zanga-zangar neman adalci a hedikwatar jam'iyyar ta ƙasa.

Da farko gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma, ya ayyana Idahosa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Edo: Manyan 'yan takara 3 daga APC, PDP da LP

Idahosa ya yi zanga-zanga a hedikwatar APC
Dennis Idahosa bai gamsu da sakamakon zaben fidda gwanin APC ba Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

Yanzu Idahosa ya sha alwashin ɗaukar matakin shari'a a kan jam'iyyar idan ba a yi adalci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya shiga tsakani ya kuma tabbatar da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ya bi gaskiya.

Menene ƙorafin Idahosa?

Da yake zantawa da manema labarai a wajen sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa, Hon. Idahosa ya bayyana cewa ya kai ƙara ga kwamitin ɗaukaka ƙara na gwamna na jam’iyyar APC.

Ya jaddada aniyar sa ta bin diddigin lamarin a tsanake kafin yin la’akari da matakin shari’a na kare haƙƙinsa a cikin jam’iyyar.

A kalamansa:

"Ban zo don in tayar da fitina ba, ni ɗan majalisa ne, amma abu ɗaya da muke so shi ne adalci, a yau na iya zama matashi, amma wataƙila ƴaƴan mambobin NWC ne gobe.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Babban malamin addini ya tura sako mai muhimmanci ga Shugaba Tinubu

"Dole mu yi abin da ya dace, idan muka ci gaba da yin abin da bai dace ba a ƙasa, ba za mu ci gaba ba.
"Don haka ina kira ga shugaban ƙasa da ya tsawatarwa NWC su yi abin da ya dace."

Ekpebholo Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Monday Okpebholo (Edo ta Tsakiya) ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Edo a inuwar jam'iyyar APC

Gwamnan jihar Cross Rivers kuma shugaban kwamitin shirya zaɓen, Bassey Otu, ne ya sanar da hakan bayan kammala tattara sakamako daga ƙananan hukumomi 18.

Asali: Legit.ng

Online view pixel