Obaseki vs Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Kujerar Gwamna a PDP

Obaseki vs Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Kujerar Gwamna a PDP

  • Mataim gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP da wani tsagin jam'iyyar ya gudanar a gidansa
  • Rahotanni sun bayyana cewa Shaibu ya samu kuri'u 301 a zaben da aka gudanar a ranar Alhamis bayan masu zaben sun saka labule
  • Wata majiya ta ce an so gudanar da zaben fidda gwanin ne a filin wasanni na Samuel Ogbemudia amma aka yi shi a gidan Shaibu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Edo - Phillip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a tunkarar zaben gwamnan Edo na 2024.

Shaibu ya lashe zaben fidda gwanin ne da kuri'u 301 yayin da dayan tsagin na Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar bai fara nasa zaben ba, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Legas: Bayan cafke shugaban LP na ƙasa, ƴar takarar mataimakiyar gwamna ta fice daga jam'iyyar

Shaibu ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a PDP a jihar Edo
Shaibu ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a PDP a jihar Edo. Hoto: @HonPhilipShaibu, @GovernorObaseki
Asali: Twitter

Shaibu ya samu kuri'u mafi rinjaye

A ranar Alhamis ne tsagin jam'iyyar da mataimakin gwamnan jihar, Shaibu, yake ya gudanar da zaben fidda gwanin a gidansa da ke Commercial Avenue, Benin City.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake bayyana sakamakon bayan tattara kuri'u, Bartholomew Moses, jami’in zaben ya bayyana cewa Shaibu ya lashe zaben da gagarumin rinjaye, Daily Trust ta ruwaito.

Tun da farko dai an ruwaito wasu wakilan jam'iyyar PDP sun je wurin da aka gudanar da zaben fidda gwani a filin wasa na Samuel Ogbemudia amma an hana su shiga.

Majiyar ta ce daga baya wakilan zaben sun koma gidan mataimakin gwamnan inda aka kada kuri'u.

Wakilan jam'iyyar sun zabi Shaibu a matsayin dan takara

Rahotanni sun ce Shaibu ya yi jawabi ga wakilan zaben inda ya shawarce su rungumi zaman lafiya, tare da yin alkawarin tattaunawa da shugaban kwamitin zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Kujerar sakataren PDP na ƙasa ta fara tangal-tangal yayin da shugabanni suka faɗi wanda suke so

Ya ce daga baya an yanke shawarar gudanar da zaben fidda gwanin na wannan tsagi wanda kuma Shaibu ya samu nasara.

Rahotanni sun ce wakilai daga kananan hukumomi 12 na jihar sun zabi Shaibu a matsayin dan takarar.

Yar takarar mataimakiyar gwamnan Legas ta fice daga LP

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa Islamiyat Oyefusi, 'yar takarar mataimakiyar gwamnan jihar Legas ta fice daga jam'iyyarta ta Labour.

Oyefusi ta ce ya zamar mata wajibi ta bar jam'iyyar saboda manufofin jam'iyyar sun saba da nata manufofin na siyasa.

Wannan na zuwa ne yayin da rikici ia jam'iyyar LP tun bayan da dakatacciyar ma'ajiyar jam'iyyar ta kasa ta zargi shugaban jam'iyyar da sace kudaden da aka tara a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.