Matsin tattalin arziki
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya ce wasu gurbatattun ‘yan siyasa ne suka haifar da faduwar darajar Naira a kasuwar duniya ta hanyar boye kudin a gidajesu.
Yayin da al'ummar Najeriya ke kokawa saboda tsadar rayuwa, wasu magidanta sun dauki matakin tserewa daga gidajensu saboda gudun daukar dawainiyar iyalinsu.
Yayin da ake zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya, Farfesa Farooq Kperogi ya yi gagarumin gargadi ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Aliyu Sani Madakin-Gini daga jihar Kano a majalisar wakilan tarayya a babban birnin Abuja ya tasa sabon gwamnan CBN a gaba game da karfafa Legas da karyewar Naira
Hukumar da ke karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci a jihar Kano ta kai samame rumbun ajiyar masu boye kayan abinci domin haifar da tsadar kaya a kasuwa.
Watsar da tsarin tallafin fetur ya jawo yunwa da wahalar rayuwa. Ministocin kasafi da na aikin gona su ka yi wa Sanatoci bayanin nan a majalisar dattawa.
Kudirin lantarki ya zama doka bayan sa hannun Bola Ahmed Tinubu a yammacin Juma’a. Dokar ta haramta raba wutar lantarki tsakanin jihohi da kasa a Najeriya.
Ministan watsa labarai, Mohammed Idris, ya ce shirin da gwamnati ta yi ba fitar da tan dubu 42 na masara, gero da garri zai karya farashin kayan abinci a kasuwanni.
Gamayyar kungiyoyi masu kare martabar damokradiyya daga jihohin Arewa 19 harda babban birnin tarayya Abuja sun ce gwamnatin Buhari ce ta haddasa tsadar rayuwa.
Matsin tattalin arziki
Samu kari