Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawari, Ta Dira Kan Rumbun Ajiyar Masu Boye Abinci

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawari, Ta Dira Kan Rumbun Ajiyar Masu Boye Abinci

  • Hukumar yaki da cin hanci a Kano, ta fara daukar mataki yayin da al'umma ke kokawa saboda tsadar rayuwa a fadin kasar
  • Jami'an hukumar sun fara bi ta kan 'yan kasuwa da ke siye kayan abinci suna boyewa da niyar siyar da su da tsada ga jama'ar gari
  • Hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Ibrahim, ne ya sanar da hakan a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar da ke karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci a jihar Kano ta shiga aiki gadan-gadan yayin da al'ummar jihar da ma na kasa ke kokawa kan tsadar rayuwar da ake ciki a yanzu.

A ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu ne jami'an hukumar suka kai samame wani rumbu da ake ajiye kayan abinci.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Gwamnatin Kano ta kai samame rumbun ajinya
Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawari, Ta Dira Kan Rumbun Ajiyar Masu Boye Abinci Hoto: @Kyusufabba/@babarh_.
Asali: Twitter

Ana dai boye kayan abinci ne a rumbun domin haifar da karancin kaya wanda zai kai ga hauhawan farashin abubuwa a kasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Abdullahi Ibrahim, ya fitar a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Ya rubuta a shafin nasa:

"Yana faruwa a yanzu haka: Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano sun fasa wani rumbun ajiya inda ake boye kayayyaki domin haifar da tsadar kaya a kasuwa."

Me shugaban hukumar ya ce?

Tun farko dai, shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji ya sha alwashin cewa zai fara kai samame inda ake ajiyar kayan abinci.

Muhyi ya ce za su fara kai samamen ne don zakulo wadanda ke boye a binci tare da daukar mataki a kansu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu a garin Kano.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wasu mazauna garin Kano don jin yadda suke fama da rayuwa a wannan lokaci.

Malama Larai Sulaiman ta ce:

"Rayuwa kam babu abin da za mu ce sai godiyar Allah, abin da talaka zai sa a bakin salati yana neman gagaransa. Wannan mataki da gwamnati ta dauka zai taimaka sosai.
"Da laifin wasu 'yan kasuwa sai ku ga suna shiga kauyuka suna siye kayan abinci suna boyewa don kawai idan ya yi tsada su fito da shi.

Malama Zainab Ummi kuwa cewa ta yi:

"Gaskiya ya kamata mahukunta da masu fada aji su shiga lamarin nan domin dai abun ya fara wuce gona da iri, ace mudun shinkafa ya doshi N2000, ga shi ba wai akwai kudin bane a gari.
"Kuma sai 'yan kasuwa sun saka tausayi a zuciyarsu domin dai kazamar riba bata sa mutum ya yi arziki, kwata-kwata zuciyar dan adam ta kyekyashe babu tausayi.

Kara karanta wannan

Kogi: An tsinci gawar daliban kwaleji a dakin kwanansu, an gano abin da ya kashe su

"Muna maraba da wannan mataki da gwamnati ta dauka na bankado duk masu boye kayan abinci don kawai su musgunawa al'umma."

Kwastam ta yi karin kudin kaya

A wani labarin, mun ji cewa hukumar Kwastam ta kara kudin shigo da kaya daga kasashen ketare sau biyu a cikin kwana daya, wannan zai shafi tattalin arziki

An rahoto cewa kaya za su kara tsada sakamakon canjin farashin shigo da kaya daga waje da gwamnati ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel