Yayin da Lamura Ke Kara Tsananta, Gwamnatin Tinubu Ta Magantu kan Cire Tallafi
- Ministan kudi Taiwo Oyedele ya kara fayyace lamarin tattalin arzikin Najeriya da hanyoyin da gwamnati ke bi domin bunkasa fannin
- Oyedele ya tabbatar da cewa gwamnatin Bola Tinubu ba za ta dawo da tallafin mai ba duk da koke-koken da ake yi kan tsadar fetur
- Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa cire tallafin mai ya rage matsin tattalin arziki tare da bude damar jawo sababbin masu zuba jari Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Paris, France - Ministan Harkokin Kudi da Tattalin Arziki na Najeriya, Taiwo Oyedele ya sake yin magana game da cire tallafin mai a Najeriya.
Oyodele ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da niyyar dawo da tallafin man fetur duk da ci gaba da korafe-korafen jama’a kan tsadar rayuwa.

Source: Twitter
Ministan ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da masu zuba jari na duniya a birnin Paris tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Tattalin arziki: Matakan da Gwamnatin Tinubu ke dauka
Ya ce gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar ci gaba da tsarin kasuwa mai ‘yanci, tare da kaucewa dawo da tallafi ko kayyade farashin kayayyaki.
“Ba za mu dawo da tallafin mai ba saboda yana haddasa tangarda ga tattalin arziki, haka kuma ba za mu saka dokar kayyade farashi ba saboda mun yarda da tsarin kasuwa."
- In ji Oyedele.
Ministan ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin kare tattalin arzikin kasar da kuma rage matsin kashe kudaden gwamnati kamar yadda aka gani a baya.
Ya kara da cewa sauye-sauyen da ake samu a kasuwar makamashi ta duniya, musamman rikice-rikicen yankunan masu arzikin mai, na ba Najeriya damar jawo sababbin masu zuba jari.

Source: Twitter
Minista ya fadi amfanin cire tallafin mai
Kalaman Taiwo Oyedele sun zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara a Najeriya kan farashin man fetur bayan cire tallafin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar tun bayan hawanta mulkin kasar a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023.
Sai dai ministan ya ce duk da sukar da ake yi, cire tallafin ya taimaka wajen rage matsin tattalin arziki tare da bai wa gwamnati damar gudanar da muhimman gyare-gyare.
Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiwatar da manufofin tattalin arziki da take ganin za su tabbatar da dorewar ci gaban kasa da jawo karin masu zuba jari daga kasashen duniya.
Ministan kudi ya kawo hanyoyin inganta tattalin arziki
Tun farko, an ji cewa Ministan kudi a Najeriya, Taiwo Oyedele ya kama aiki a hukumance domin inganta tattalin arziki bayan karɓar ragama daga hannun tsohon minista Wale Edun.
Ministan ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin sauye-sauyen da ake yi sun taba rayuwar talakawa kai tsaye ta hanyar gyara tsarin haraji.
Oyedele ya jaddada cewa ba zai tsaya ga kyawawan manufofi a takarda ba, sai dai zai mayar da hankali ne wajen samar da sakamako na gani da ido.
Asali: Legit.ng

