Tsohon Gwamna a Arewa Ya Tona Asirin Wadanda Ke da Hannu a Faduwar Darajar Naira

Tsohon Gwamna a Arewa Ya Tona Asirin Wadanda Ke da Hannu a Faduwar Darajar Naira

  • Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya ce wasu gurbatattun ‘yan siyasa ne suka haifar da faduwar darajar Naira a kasuwar duniya
  • Ya yi ikirarin cewa 'yan siyasar na kwashe daloli suna ajiyewa a gidajensu da kuma asusu na kasashen waje kawai don son kan su
  • Isa Yuguda ya kuma yi nuni da cewa rashin tsaro na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya magantu kan faduwar darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, da kuma tsadar rayuwa a Najeriya.

Ya ce hakan ya samo asali ne sakamakon wasu gurbatattun ‘yan siyasa da ke kwashe daloli suna ajiyewa a gidajensu da kuma asusu na kasashen waje.

Kara karanta wannan

AFCON: Tinubu ya aika muhimmin sako ga Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe

Wadanda ke da hannu a faduwar darajar Naira
Isa Yuguda ya fadi wadanda ke da hannu a karyewar darajar Naira akan dalar Amurka. Hoto: Labari daga Bauchi.
Asali: Facebook

Abin da ya jawo karancin abinci a Najeriya

Ya kuma ce daya daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta shi ne rashin tsaro, tare da kuma boye kayan abinci da ‘yan Najeriya ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yuguda ya bayyana haka ne a wajen taron magance talauci a Arewacin Najeriya da kungiyar Arewa New Agenda, ANA ta hada a karshen mako a Abuja.

A cewar tsohon gwamnan, magance fatara da talauci a Arewacin Najeriya na bukatar daukar matakan da suka dace, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Isa Yuguda ya ba gwamnati shawarar mafita

Ya yi kira ga tawagar tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Tinubu da su fito da tsare-tsare da za su magance kalubalen tattalin arzikin kasar nan.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba sosai tare da saka hannun jari a fannin tsaro domin tunkarar kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Da yake karin haske game da janye tallafin man fetur, tsohon gwamnan ya ce ya zama dole saboda yadda ake tafka almundahana a harkar man fetur.

Gwamnati za ta karya farashin kayan abinci

A makon da ya gabata, Legit Hausa ta ruwaito maku ce gwamnatin tarayya ta dauki matakai na karya farashin kayan abinci a kasuwannin Najeriya.

Daga cikin matakan da ta dauka akwai fitar da ton dubu 42 na kayan abinci daga rumbun gwamnati don sayar da shi a farashi mai sauki.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne biyo bayan hauhawar farashin kayan abinci sakamakon karyewar darajar Naira wanda ya haddasa tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel