Gwamnatin Kano Ta Bayyana Alfanun da Aka Samu Sakamakon Rufe Rumbunan Masu Boye Kayan Abinci

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Alfanun da Aka Samu Sakamakon Rufe Rumbunan Masu Boye Kayan Abinci

  • Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙiɓda cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta faɗi dalilin dira kan wasu rumfunan ajiya da ake ɓoye abinci
  • Shugaban hukumar Muhuyi Magaji, ya bayyana cewa sun rufe rumbunan saboda yadda farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zaɓi
  • Muhuyi ya kuma yi nuni da cewa hakan da suka yi ya haifar da ɗa mai ido domin farashin kayan abinci yanzu ya daidaita a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano ta bayyana dalilin da ya sa ta rufe rumfunan ajiya da ake zargi da ɓoye muhimman kayayyaki.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, shugaban hukumar Muhuyi Magaji, ya ce matakin ya haifar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Ƴan kasuwa sun rage farashin kayan masarufi, talakawa zasu samu sauƙin sayen abinci

Dalilin rufe rumbunan ajiya a Kano
Gwamnatin Kano ta fadi dalilin rufe rumbunan boye abinci Hoto: @Kyusufabba, @babarh
Asali: Twitter

Meyasa gwamnatin Kano ta rufe rumbunan ajiya?

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Dalilin da ya sa muka yi haka shi ne, ana samun ƙarin farashin kayan abinci nan take wanda ya kawo damuwa ga al’ummar Kano.
"Mun samu korafe-korafen jama’a, mun sami shawarwarin jama’a ga gwamnati kuma mun fuskanci matsin lamba musamman saboda mun taɓa yin hakan a baya yayin COVID-19 kuma mun samu sakamako mai kyau."
"Kafin mu yi hakan, mun gayyaci ƴan kasuwa zuwa ofishinmu, kuma game da Dawanau, na ziyarci kasuwar da kaina, na shaida musu cewa, za mu dira kan masu ɓoye kayayyaki.
"Zan gaya muku cewa a Kano an samu sakamako mai kyau, saboda mun daidaita farashin yanzu haka da na ke magana da ku.

Shugaban ya ƙara jaddada suna da hujja daga ɓangaren shari'a wacce ta sanya suka dira kan rumbunan, inda ya ce a doka ɓoye abinci laifi ne.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

An Rage Farashin Kayayyaki a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan kasuwar da ke siyar da kayan masarufi sun yanke shawarar rage farashin kayayyakin su a jihar Kano.

Ƴan kasuwar dai sun cimma wannan matsayar ne biyo bayan rufe wasu rumbunan da ake ɓoye abinci da hukumar PCACC ta yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel