Abu Ya Lalace: Maza Sun Fara Guduwa Suna Barin Gidajensu Saboda Tsadar Rayuwa a jihar Arewa

Abu Ya Lalace: Maza Sun Fara Guduwa Suna Barin Gidajensu Saboda Tsadar Rayuwa a jihar Arewa

  • Yayin da ake fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a Najeriya magidanta sun fara daukar mataki mai daga hankali
  • Wani rahoto ya nuna cewa kimanin magidanta 105 ne suka yi kaura daga gidajensu saboda gudun daukar dawainiyar iyalinsu a jihar Gombe
  • Hukumar kare 'yancin dan adam ta kasa, reshen jihar Gombe ce ta tabbatar da hakan bisa ga korafe-korafen da ta samu a bara

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Al'ummar Najeriya na cikin wani mawuyacin hali, inda suke fama da matsi da tsadar rayuwa.

Lamarin ya kara kamari ne tun daga watan disamban bara inda kaya suka yi tashin gauron zabi a kasuwa.

Bincike ya gano cewa janye tallafin man fetur da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, ya taimaka wajen janyo hauhawan farashin kayayyakin amfanin yau da kullum.

Kara karanta wannan

Hare-haren 'yan bindiga: Shugaba Tinubu ya amince da aiwatar da wani abu 1 a jihar Arewa

Kasuwar hatsi
Abu Ya Lalace: Maza Sun Fara Guduwa Suna Barin Gidajensu Saboda Tsadar Rayuwa a jihar Arewa Hoto: Trust Radio
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maza 105 ne suka bar gida - Hukumar kare 'yancin dan adam

Kamar yadda VOA Hausa ta ruwaito, hukumar kare 'yancin dan adam ta kasa, reshen jihar Gombe, ta bayyana cewa sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da shi, magidanta sun fara barin gidajensu.

Kakakin hukumar, Mista Ali Alola Alfinti, ya ce daga cikin korafe-korafe 280 da suka samu a bara, magidanta 105 ne suka yi kaura daga gidajensu saboda gudun daukar dawainiyar iyalinsu.

Wani magidanci mai suna Garba Tela Herwa Gana Wudil Gombe, wanda ya shafe tsawon shekaru 50 da aure ya ce yi tsokaci kan lamarin.

Garba ya ce:

"Toh wallahi ina tabbatar maka, magidanta a abokaina ma tukun, a unguwarmu nan ma akwai wadanda yanzu sun tafi.
"Yanzu haka maganar nan ma da nake da kai wallahi ga wani yaro nan ma, na zo ina tambayarsa ma, yace ya zo neman sadaka ne nace daga ina?, yace mamansa ne tace ya zo ya dunga yawo shine idan sun yi bara shine ake samun dan abin da za a taba.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

"Saboda haka wahalar da ake sha ya wuce duk inda mutum yake tsammani. Yanzu kwanan nan yan unguwarmu ma kawai wadanda suka bar unguwar na rantse suna da yawa."

Mata da yara basu san babu ba, Magidanci

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani magidanci mai suna Malam Abubakar Gawun, wanda ya mallaki yara shida da matan aure biyu kan halin da ake ciki a yanzu.

Mallam Gawun ya ce:

"Lallai halin da ake ciki yanzu ya kai makura. Ko ni nan wasu lokutan na kan ji kamar na gudu na bar gida abun ya yi yawa. Da wanne mutum zai ji, dawainiyar makaranta, na abinci ko na asibiti?.
"Komai ka taba a kasuwa kudi ne, ga shi su dama mata da yara basu san babu ba kullun dai burinsu ka kawo, duk ranar da aka samu akasi babu zaman lafiya, toh ya mutum ya iya.
"Sai dai kuma duk da wadannan matsalolin, bana tunanin barin gida zai zamo maslaha, don duk inda za ka ce hankalinka ba zai zama a kwance ba. Allah ya iya mana."

Kara karanta wannan

Bayan sace 'yan kai amarya, 'yan bindiga sun sake yin awion gaba da mutane a jihar Arewa

An gargadi Tinubu saboda tsadar rayuwa

A wani labarin, Farfesa Farooq Kperogi, ya gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu cewa "hauhawan farashin kaya da ke faruwa a Najeriya ba bisa ka'ida ba" babban barazana ne ga zamantakewar kasar.

Shahararren marubucin ya ce zanga-zangar da ya gudana a jihohin Neja, Kano da Osun a baya-bayan nan, alamun gargadi ne ga gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng