Ministocinsa 2 Sun Je Majalisa, Sun Soki Tsari da Manufofin Gwamnatin Bola Tinubu

Ministocinsa 2 Sun Je Majalisa, Sun Soki Tsari da Manufofin Gwamnatin Bola Tinubu

  • Majalisar dattawa ta gayyaci wasu daga cikin ministocin gwamnatin tarayya domin yi masu bayani
  • Hakan ya zama tilas ne la’akari da halin da tattalin arziki ya shiga musamman ta fuskar karyewar Naira
  • Ministocin kasafi da na aikin gona sun yi sun soki cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi a Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministoci biyu wanda yanzu haka su na da kujeru a majalisar zartarwa ta kasa, FEC, sun soki tsare-tsaren da aka kawo.

Rahoton Tribune ya fahimtar da mu cewa ministocin tarayyan ba su gamsu da cire tallafin man fetur da yadda aka karya Naira ba.

Tinubu
Ministan kasafi a gwamnatin Bola Tinubu Hoto: Buhari Sallau, Nigerian Senate
Asali: Facebook

Bankin CBN ya saki Dalar Amurka ta nemawa kan ta farashi a Najeriya, matakin nan ya jawo karyewar Nairan da ba a taba gani ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar Bagudu da Sanata Abubakar Kyari suna ganin akwai gyara a manufofin.

Ministocin Tinubu a gaban Sanatoci

A jiya Sanata Atiku Bagudu da Kyari wadanda su ne Ministocin kasafi da na harkar noma su ka zauna da Sanatoci a majalisar dattawa.

Ministocin sun shaidawa kwamitocin kasafi, harkar banki da na tattalin arziki yadda janye tallafin man fetur ya jawo karin tsadar rayuwa.

Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin na Bola Tinubu ya ce tashin kudin fetur yana nufin karin tsadar kudin zuwa gonaki.

Shi kuwa Abubakar Kyari ya ce karya Naira da gwamnan CBN ya yi, ya yi sanadiyyar bata fashin kayan amfanin gona a halin yanzu.

Rahoton ya ce Ministan yana zargin kayan abinci sun fi araha a makwabtan Najeriya.

Tattalin arziki: Tusa ta karewa bodari?

A jawabin da ya yi wa kwamitocin majalisar, Olayemi Cardoso ya nuna dole ‘yan Najeriya su rage kwadayin neman kudin waje.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi da Kiristoci Sun Hada Kai, Sun Taso Gwamnati Gaba Kan Tsadar Rayuwa

Vanguad ta ce gwamnan ya ce tsarinsu ya fara aiki domin an shigo da $1bn, sai dai ya ce babu dabarar da ta rage wajen farfado Naira.

Tinubu ya yi daidai wajen cire tallafi?

Tsohon shugaban PACAC, Farfesa Itse Sagay ya ce gaggawar yadda aka janye tallafin fetur a haifar da wahala a mulkin Bola Tinubu.

Da an bi shawarar Sagay, ya kamata a ce an jira na tsawon watanni shida domin za a fara tace mai a cikin gida, daga nan a cire tallafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng