Jihar Benue
Wasu 'yan ta'adda da ba a san ko su waye ba sun kai sababbin hare-hare a jihar Benue. Miyagun sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Dan Majalisar Wakilai, Hon. Terseer Ugbor ya caccaki gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Hyacinth Alia da rashin jawo kowa a jiki a yaƙi da matsalar tsaro.
Majalisar wakilai ta ba gwamnonin Benue da Zamfara wa'adin mako 1 su bayyana gabanta. Lauyoyi sun shigar da ƙara kan dakatar da 'yan majalisa ba bisa ƙa'ida ba.
Rundunar tsaro a Najeriya ta ce makiyayan kasashen ketare ne ke kai hari a jihohin Benue da Plateau, inda suka shigowa ƙasar ta iyakoki masu rauni.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Benue. 'Yan bindigan sun hallaka wani basarake lokacin da yake aiki a gonarsa.
Majiyoyi sun ce wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani jami’in ‘yan sanda da wani mutum a kauyen Ikyac-Gev da ke Makurdi a jihar Benue.
'Yan bindiga sun kashe jigon APC da wasu mutum uku a Benue a wani harin kwantan bauna da suka kai garuruwa biyu. An ce wannan ne hari na biyu a cikin makonni biyu.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa akwai wani shiri da ake kullawa domin raba shi da kujerarsa. Ya ce masu wannan shirin ba za su yi nasara ba.
Lauyoyi sun nemi majalisar tarayya ta kwace ikon majalisun Benue da Zamfara saboda dakatar da 'yan majalisu 23. Sun hango abin da zai faru idan ba a dauki mataki ba.
Jihar Benue
Samu kari