Babban Basarake Ya Gayawa Tinubu Hakikanin Abin da Ke Faruwa a Benue
- Mai martaba Tor Tiv na jihar Benue, James Ayatse ya yi bayani yayin taron masu ruwa da tsaki kan matsalar rashin tsaro
- James Ayatse ya gayawa Shugaba Bola Tinubu cewa ana ba da bayanai ba daidai ba kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a jihar
- Sarkin kasar Tiv ya bayyana cewa rikicin da ake yi a Benue wani shiryayyen shiri ne da aka tsara don raba mutane da filayensu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Tor Tiv, na jihar Benue, James Ayatse, ya ƙaryata iƙirarin da ke cewa kashe-kashen da ake yi a Benue sakamakon rikici ne tsakanin makiyaya da manoma.
Mai martaba James Ayatse bayyana irin waɗannan ikirarin a matsayin yaɗa ƙarya da bayanan da ba su dace ba.

Asali: Twitter
Tashar Channels tv ta ce ya bayyana hakan ne a yayin taron da aka gudanar tsakanin Shugaba Bola Tinubu da manyan masu ruwa da tsaki jihar Benue a ranar Laraba, 18 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tor Tiv ya yi wa Bola Tinubu jawabi
James Ayatse ya ce irin wannan bayani da ake yaɗawa ya sa wasu ke ba al’ummar Benue shawarar su ci gaba da nuna haƙuri tare da karɓar baƙi.
Ya bayyana cewa kashe-kashen ba rikice-rikicen manoma da makiyaya ba ne, illa dai shirin kisan kare dangi da aka tsara tsaf tare da yunƙurin mamaye ƙasa, wanda ƴan ta'adda makiyaya da ƴan bindiga ke aiwatarwa a jihar tsawon shekaru da dama.
"Muna da damuwa sosai game da yadda ake yaɗa ƙarya da kuma bayar da bayanan da ba daidai ba game da halin tsaro a jihar Benue."
"Mai girma shugaban ƙasa, ba rikicin makiyaya da manoma bane, ba rikicin ƙabilanci bane, ba rikicin ramuwar gayya ba ce."
"Wannan yaɗa ƙaryar da rashin fahimta ne ya sa wasu ke bayar da shawara irin su ‘ku yi haƙuri, ku sasanta, ku koyi zaman lafiya da maƙwabta’."
"Abin da muke fuskanta a nan Benue wani shiri ne da aka tsara da gangan, shiri ne na yaƙi da kisan ƙare dangi da kuma ƙwace ƙasa ta hanyar farmakin makiyaya ƴan ta'adda, wanda ke ci gaba da gudana tun shekaru da dama da suka wuce kuma yana ƙara muni a duk shekara."
"Idan an gano cuta ba daidai ba, maganinta ma ba zai yi daidai ba. Don haka abin da muke fuskanta ya fi yadda ake tunani muni. Ba wai koyon zaman lafiya da makwabta ba ne kawai, muna cikin yaki ne."
- James Ayatse

Asali: Twitter
Majalisa ta buƙaci mutanen Benue su kare kansu
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin Benue, ta koka kan halin rashin tsaro da ya addabi jihar.
Majalisar ta danganta majalisar kan halin ko in kula da gwamnati take nunawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ta buƙaci mutanen jihar da su ci gaba da sanya ido tare da ɗaukar matakan kare kansu daga hare-haren ƴan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng