'Sau 130 Ina Kiran Ribadu': Malamin Addini Ya Faɗi Abin da Hadimin Tinubu Ya Yi Masa
- Fasto Elijah Ayodele ya bayyana yadda ya yi ta kiran hadimin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu game da hare-hare
- Malamin addinin kiristan ya kira waya sau 130 yana kiran Ribadu don ya gargaɗe shi game da harin Benue, amma ba a saurare shi ba
- Ya bayyana cewa ya rubuta wasiƙa da aika saƙonni, ya kai ziyara ofishin Ribadu, amma an hana shi shiga har mai faruwa ta faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban cocin 'Evangelical Spiritual', Elijah Ayodele, ya bayyana yadda yake kokarin dakile hare-hare a Najeriya.
Faston ya bayyana yadda ya kira mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, sau da dama domin ya gargaɗe shi kan hare-hare.

Asali: Facebook
Ana zargin sakacin Ribadu a harin Benue
Ayodele ya ce sau 130 yana kiran Ribadu kafin a kai harin Benue, amma bai samu amsa ba, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya ce ya gani a mafarki makonni kafin faruwar lamarin, inda ya ambaci hakan a cikin littafinsa na wahayi na shekara-shekara.
Fasto Ayodele ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya nemi Nuhu Ribadu kai tsaye shi ne domin ya isar da saƙon da Allah ya ba shi.
Ya ce amma abin takaici, an yi biris da shi har sai da abin da ya faru ya faru yanzu an zo ana ta maganganu kan lamarin.
Ya ce:
“Na kira Nuhu Ribadu sau 130 domin na gargaɗe shi game da kisan Benue tun kafin su faru, domin a dakile su, amma idan an ɗora mutanen da ba sa jin tsoron Allah a kan mulki, irin waɗannan abubuwan ne ke faruwa.
"Na aika masa da saƙonni, amma bai taɓa amsawa ba. Ina ganin shi ya kamata a dorawa laifin abin da ya faru a Benue.”

Asali: Facebook
Yadda aka wulanƙanta Faston a ofishin Ribadu
Ayodele ya bayyana rashin jin daɗinsa kan Ribadu, inda ya ce ya je ofishinsa amma aka ƙi karɓarsa, ya kuma rubuta wasiƙa amma ba a duba ta ba.
“Watakila yana ganin ina son karɓar kuɗi ne daga gare shi, kuma ina mamakin irin kuɗin da zai bani da ban riga na mallaka ba.
"Na je ofishinsa, amma aka kore ni. Na ci gaba da rubuta wasiƙa domin Allah baya son a zubar da jinin bayinsa, amma waɗannan shugabanni abin takaici ne.”
- Cewar Ayodele
Har ila yau, Ayodele ya ce matsalar Benue ta fi ƙarfin gwamna, inda ya shawarci shugabanni su rika girmama Allah domin a samu nasarar tafiyar da mulki yadda ya kamata, Daily Post ta tabbatar.
Fasto Ayodele ya gargadi Muhammadu Sanusi II
A baya, kun ji cewa limamin coci, Elijah Babatunde Ayodele, ya bayyana wahayin da aka yi masa kan wasu manyan mutane a Najeriya.
Fasto Ayodele ya yi kaurin suna wajen hasashen abin da zai faru a nan gaba, inda ya taɓo batun sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II.
Hakan ya biyo bayan fadawar jihar Kano a cikin rikicin sarauta tun lokacin da majalisar dokoki ta rusa masarautu biyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng