Shugaba Tinubu Ya Bayyana Darasin da Yake Koya daga Masu Sukarsa

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Darasin da Yake Koya daga Masu Sukarsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓo batun masu zuwa kafafen watsa labarai su soki gwamnatinsa da shi kansa
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa yana koyon darussa kan shugabanci daga wajen mutanen da suke sukarsa
  • Shugaban ƙasan ya nuna cewa masu sukarsa ba su ganin abin da yake yi, domin ko me zai yi sai sun ci masa mutunci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana darussan da yake koya daga wajen masu sukarsa.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana koyan darussa na shugabanci daga masu sukarsa da ke bayyana ra’ayoyinsu a kafafen watsa labarai.

Shugaba Tinubu ya yi magana kan masu sukarsa
Shugaba Tinubu ya ce yana koyon darasi daga wajen masu sukarsa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wajen taro da masu ruwa da tsaki kan matsalar rashin tsaro a Benue, wanda aka gudanar a birnin Makurdi, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kai ziyara jihar Benue ne, bayan da aka samu hare-haren makiyaya masu ɗauke da makamai a ƴan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 100.

Me Tinubu ya ce kan masu sukarsa?

Shugaba Tinubu ya ce yana ɗaukar korafe-korafe da ra’ayoyin jama’a da muhimmanci, yana kuma koya daga cikin sukar da ake yi masa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

“Ko mene ne zan yi, za su ci min mutunci. Ina karanta jaridu kuma ina koya daga cikin sukar da su ke yi, domin ba zan iya ganin komai da kaina ba."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya yi kalamai kan Gwamna Alia

Yayin da yake magana da Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue, Tinubu ya ce ba a zaɓi gwamnan domin ya riƙa binne gawarwakin mutanensa ba.

Ya bayyana cewa zai haɗa kai da shi domin ganin an samu zaman lafiya a jihar Benue.

“An zaɓe ka ƙarƙashin tutar masu kishin ci gaba domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da lumana, domin mu samu damar zuwa mu ƙaddamar da ayyuka, mu taya ka murna kan abubuwan alheri da farin ciki."
“Ba a zaɓe ka don ka riƙa birne mutane ba, ko samar marayu da gidajen marayu ba, ko kuma nuna tausayi ga zawarawa ba. Za mu yi aiki tare da kai domin cimma zaman lafiya."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya kai ziyara a jihar Benue
Shugaba Tinubu ya yi magana kan rashin tsaro a Benue Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Tinubu ya kuma yi raddi ga abokan hamayyar siyasar Gwamna Alia.

“Abokan gabar ka na siyasa ba sa so ka yi nasara. Yanzu ko ka fahimci haka?”

- Shugaba Bola Tinubu

Ya yi kira ga shugabanni a fadin jihar Benue, da su haɗa kai domin kawo ƙarshen rikici da kuma gina sabuwar amincewa tsakanin al’ummomi.

Basarake ya yi wa Shugaba Tinubu jawabi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai martaba Tor Tiv na Benue, James Ayatse, ya yi bayanai ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalar rashin tsaron jihar.

Mai martaba James Ayatse ya bayyana cewa ana ba da bayanai waɗanda suke ba daidai ba, dangane da matsalar rashin tsaron wacce ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.

Babban basaraken ya nuna matsalar rashin tsaron Benue ba rikicin makiyaya da manoma ba ne, fa ce wani shiryayyen shiri na yin kisan ƙare dangi da ƙwace filayen mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng