Jihar Benue
Kotun Koli da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru da Chukwuma Odii na PDP.
Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnonin jihohin Benue da Ebonyi a yau Litinin 8 ga watan Janairu a babban birnin Tarayya, Abuja.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Gwamna Hyacinth Alia sun samu sabani kan dakatar da zaben fidda gwani na zaben cike gurbi a jihar Benue.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Benuwai ta tabbatar da cewa wasu manyan shugabanninta guda biyu sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki, ta musu fatan alheri.
Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya buƙaci kowane ɓangare da sabani ya shiga takaninsa da ɗan uwansa a jihar Benuwai su haɗa kai wuri ɗaya.
Rikici na neman barkewa tsakanin ƴan majalisar tarayya na jihar Benuwai da Gwamna Hyacinth Alia, sun zargi gwamnan da mulkin kama karya da ruguza APC.
Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue ya yi martani kan zargin mulkin kama-karya da 'yan Majalisun Tarayya a jihar Benue inda ya ce shi ya taimakawa APC ta ci mulki.
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya shiga taron sirri da babban hafsan tsaron Najeriya a hedkwatar tsaro da ke Abuja kan batun tsaro a lokacin kirsimeti.
Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan jita-jitar sake bullar cutar annobar 'Korona' a Najeriya inda ta ce babu kamshin gaskiya kan labarin da ake yada wa.
Jihar Benue
Samu kari