An Maka INEC a Kotu kan Zargin Gwamnonin APC da Yashe Biliyoyi domin Kamfen 2027

An Maka INEC a Kotu kan Zargin Gwamnonin APC da Yashe Biliyoyi domin Kamfen 2027

  • Kungiyar SERAP ta kai hukumar zaben mai zaman kanta, INEC kotu tana neman ta binciki gwamnonin APC
  • Ana zargin gwamnonin da karkatar da biliyoyin Naira daga kudaden FAAC domin yakin neman zaben 2027
  • Kungiyar ta bukaci kotu ta tilasta INEC ta nemi APC da gwamnoni su bayyana gudummawar da aka bayar, masu bayarwa da kuma asalin kudaden

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar SERAP ta shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tana kalubalantar Hukumar Zabe ta INEC.

Ƙungiyar ta kai karar saboda abin da ta bayyana a matsayin gazawar hukumar wajen binciken wasu zarge-zarge masu nauyi.

SERAP ta maka INEC a kotu game da gwamnonin APC
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X a yau Lahadi 12 ga watan Yulin 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

APM ta ɗauko batun yadda Bola Tinubu ya kashe kuɗin tallafin mai da ya cire a Najeriya

Kungiyar ta yi ikirarin cewa wasu gwamnonin jam'iyyar APC sun karkatar da kusan naira biliyan 800 daga rabon kudaden FAAC domin tallafa wa yakin neman sake zaben Shugaba Bola Tinubu.

Ta ce an shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1426/2026 makon da ya gabata domin neman a binciki zargin.

SERAP ta ce ta dogara da rahotannin kafafen yada labarai da ke zargin cewa gwamnonin APC suna ware wani bangare daga kudaden FAAC da suke karba duk wata.

Kungiyar ta kuma gabatar da wani ra'ayi da marubuci Festus Adedayo ya wallafa a Premium Times a ranar 17 ga Mayu, 2026, a matsayin hujjar goyon bayan karar.

Rahoton ya yi zargin cewa an ware kusan naira biliyan 800 domin yakin neman zaben Tinubu na shekarar 2027, tare da cewa an samu karkatar da wadannan kudade.

SERAP na neman umarnin kotu wanda zai tilasta INEC ta gudanar da cikakken bincike kan wadannan zarge-zarge da suka shafi kudaden yakin neman zabe.

Kungiyar ta kuma bukaci kotu ta umarci INEC ta tilasta APC da gwamnoninta su bayyana duk gudummawar da aka bayar, sunayen masu bayarwa da kuma halalcin asalin kudaden.

Kara karanta wannan

An kuma samun matsala a shari'ar da aka nemi ƙwace kadarorin Malami a Abuja

Haka kuma, SERAP na son INEC ta fara nazari da bincike kan yadda jam'iyyun siyasa da 'yan takara ke bin tanadin Sashe na 91 na Dokar Zabe.

Kungiyar ta ce zarge-zargen sun haifar da damuwa kan gaskiya a harkokin kudaden siyasa, adalcin zabe da kuma hakkin 'yan Najeriya na shiga mulki cikin 'yanci.

A cewar SERAP, rashin bayyana yadda ake tara da kashe kudaden siyasa na kara bude kofar cin hanci da rashawa tare da raunana sahihancin dimokuradiyya.

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Kehinde Oyewumi, sun bayyana cewa amfani da kudaden jama'a wajen siyasa zai iya jefa sahihancin zaben shekarar 2027 cikin hadari.

Kungiyar ta ce girman kudaden gwamnati da raunin tsarin sa ido da bayyana bayanai sun isa su sa INEC ta yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta.

SERAP ta jaddada cewa Sashe na 91 na Dokar Zabe ya bai wa INEC ikon kayyade iyakar gudummawar da mutum ko kungiya za su iya bayarwa.

Dokar ta kuma bai wa INEC ikon tilasta bayyana wadanda suka bayar da gudummawa, asalin kudaden da kuma daukar matakin hukunta masu karya doka.

Kara karanta wannan

"Sauran jam'iyyu suna bacci," Akpabio ya fadi yadda Tinubu zai lashe zaben 2027

A karkashin dokar, jam'iyyar da ta karbi gudummawar da ta wuce ka'ida na iya fuskantar tarar naira miliyan 10 tare da kwace kudaden da suka zarce iyaka.

Haka kuma, duk wanda ya bayar da gudummawar da ta haura iyakar doka zai iya fuskantar tara har sau biyar na adadin kudin da ya bayar fiye da ka'ida.

SERAP ta ce idan zarge-zargen sun shafi yiwuwar amfani da kudaden gwamnati wajen harkokin siyasa, wajibi ne INEC ta gudanar da bincike cikin gaggawa.

Kungiyar ta kara da cewa gazawar INEC wajen aiwatar da dokokin da suka shafi kudaden yakin neman zabe na iya rage amincewar jama'a da tsarin zaben Najeriya.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, kotu ba ta sanya ranar da za a fara sauraron karar da SERAP ta shigar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.