Arewa
Wani dan bindiga ya gamu da tsautsayi yayin da ya je sace makwabcinsa, Alhaji Mohammed Makasudi a jihar Neja, mai gidan ya harbe shi a kafa yayin sace shi.
Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya karyata jita-jitar cewa su na tattaunawa da 'yan bindiga a asirce a Zamfara kamar yadda Gwamna Dauda Lawal ya yi zargi.
Tsohuwar minista a lokacin gwamnatin Buhari, Sadiya Farouk ta shiga jerin masu gangami don ceto daliban da aka sace a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke jihar Zamfara.
Masu garkuwa sun sace Kwamishinan yada labarai da al'adu a jihar Benue, Matthew Abo a daren jiya Lahadi 24 ga watan Satumba a gidansa da ke Zaki-Biam.
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya ware makudan kudade don bai wa matasa masu bautar kasa musamman wadanda aka tura makarantu don farfado da ilimi.
Gwamnan jihar Zamfara ya ce za a bindige duk wanda aka gani yana hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Alkalan kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kano sun bayyana yadda 'yan ta'addan Kwankwasiyya su ka kore su a Kano tare da musu barazana na rayukansu.
Wasu yan daba sun bankawa motoci akalla biyu wuta yayin da suka kai farmaki gidan jigon jam'iyyar SDP a jihar Kogi, Abdul Yusuf Amichi da daddare.
Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta cafke wani da ake zargi da kashe dan jarida Hamisu Danjinga da aka samu gawarsa a bayan gidansa wanda ake zaton sace shi.
Arewa
Samu kari