Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Dan Jarida A Jihar Zamfara

Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Dan Jarida A Jihar Zamfara

  • Rundunar 'yan sanda a Zamfara sun kama wani daga cikin wadanda ake zargi da kisan dan jarida, Hamisu Danjinga
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Yazid Abubakar shi ya bayyana haka a yau Juma'a 22 ga watan Satumba a Gusau
  • Yazid ya ce an kama wani mai suna Mansur Haruna da wayar marigayin a yau Juma'a

Jihar Zamfara - Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta kama wani da ake zargi da kisan dan jarida, Hamisu Danjinga.

Rundunar ta ce an kama wanda ake zargin ne mai suna Mansur Haruna da wayar hannun marigayin a jihar.

Yan sanda sun cafke wani da ake zargi da kashe dan jarida
An cafke wani da ake zargi da kisan dan jarida. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Yaushe aka kashe dan jaridan a Zamfara?

Danjinga ya bata ne a sanar Asabar 16 ga watan Satumba inda ake tunanin 'yan bindiga ne su ka yi garkuwa da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kammala Binciken Gawar Fitaccen Mawakin Nan Da Ka Tono Daga Ƙabari, Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Laraba ne 20 ga watan Satumba aka samu gawar Hamisu a kusa da kofar gidansa a cikin ramin bahaya.

An samu marigayin ne a Unguwar Yelwa Samaru da ke birnin Gusau babban birnin jihar, cewar Tribune.

Meye martanin 'yan sanda kan kisan dan jaridan?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Yazid Abubakar shi ya bayyana haka a yau Juma'a 22 ga watan Satumba.

Ya ce rundunar za ta tura wanda ake zargin kotu kan zargin hadin baki da kuma kisan kai.

Sanarwar ta ce:

"A ranar 20 ga watan Satumba mun samu labarin bacewar wani dan jarida tun ranar Lahadi 17 ga watan Satumba wanda shugaban kungiyar 'yan jaridu, Ibrahim Musa ya kawo rahoto.
"Mu na mai tabbatar muku cewa kafin wannan rahoto babu wani daga cikin iyalansa da ya kawo rahoto ga hukumar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rundunar 'Yan Sanda A Kano Ta Yi Garambawul A Dokar Hana Fita Da Ta Kafa, Bayanai Sun Fito

Har ila yau, a ranar kuma an samu gawar marigayin a kusa da gidansa a ramin bahaya da yammaci kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, TVC ta tattaro.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Yayin samame an kama wani Mansur Haruna mai shekaru 35 da wayar hannu kirar Gionee karama wanda yanzu haka ana kan bincike."

An samu gawar dan jarida a jihar Zamfara

A wani labarin, an shiga jimami yayin da aka tsinci gawar fitaccen dan jarida, Hamisu Danjinga a cikin rami.

Kungiyar 'yan jarida a jihar sun kai rahoton ga hukumar 'yan sanda don bincike da daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel