Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani Na APC, Ta Yi Fatali Da Karar PDP A Kaduna

Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani Na APC, Ta Yi Fatali Da Karar PDP A Kaduna

  • Kotun zaben jihar Kaduna ta tabbatar da Uba Sani a matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna
  • A jiya ne aka yanke hukunci tsakanin Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC da kuma Isa Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP
  • An samu rudani a hukuncin kotun inda ko wane bangare ke ikirarin samun nasara a kotun bayan yanke hukunci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kaduna ta tabbatar da Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar.

Da ta ke yanke hukunci, kotun ta tabbatar da cewa Uba Sani shi ne halastaccen zababben gwamna.

Hukuncin kotun zaben jihar Kaduna tsakanin APC da PDP
Kotun Zabe Ta Yi Hukunci A Jihar Kaduna. Hoto: Uba Sani, Isa Ashiru Kudan.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yi tsakanin APC da PDP a Kaduna?

Isa Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP na kalubalantar zaben gwamnan jihar da cewa an tafka magudi da kura-kurai.

Kara karanta wannan

Kaduna: Isah Ashiru Ya Karyata Uba Sani, Ya Fadi Gaskiyar Hukuncin da Kotu Ta Yanke

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC ta tabbatar da Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris, Daily Trust ta tattaro.

Amma Ashiru Kudan da jam'iyyar PDP sun ki amincewa da sakamakon inda su ka runtuma zuwa kotu don neman hakkinsu.

Gamayyar alkalan guda uku wanda Mai Shari'a, Victor Oviawe ya jagoranta sun gabatar da shari'ar ce ta manhajar 'Zoom'.

Rudani daga jam'iyyun APC da PDP a Kaduna

An samu rudani yayin wannan shari'ar inda gidajen jaridu da dama su ka sanar da cewa an kwace kujerar Gwamna Uba Sani.

Ko wane bangare daga cikin jam'iyyun sun nuna su ne da nasara a shari'ar da aka yi a jihar.

Lauyan APC, Sani Musa ya ce sun yi murna da hukuncin kotu inda ya ce babu bukatar daukaka kara saboda su ne da nasara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Yayin da lauyan PDP, Barista Baba Aliyu a martaninshi ya ce kotu ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, Premium Times ta tattaro.

Uba Sani da Isa Ashiru Kudan duk sun fitar da sanarwa inda su ke ikirarin nasara a shari'ar kotun.

Kotun zabe a Kaduna ta shirya yanke hukunci a manhajar 'Zoom'

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kaduna ta shirya yanke hukunci a manhajar 'Zoom'.

Kotun ta dauki wannan matakin ne don kaucewa matsaloli yayin gudanar da shari'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel