Kotun Kararrakin Zabe A Jihar Kaduna Ta Shirya Yanke Hukunci Ta Manhajar 'Zoom'

Kotun Kararrakin Zabe A Jihar Kaduna Ta Shirya Yanke Hukunci Ta Manhajar 'Zoom'

  • Kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a jihar Kaduna ta shirya yanke hukunci a yau din nan
  • Kotun ta bi sahun jihar Kano don gudanar da shari'ar ta manhajar 'Zoom' don gudun matsaloli
  • Dan takarar jam'iyar PDP, Isa Ashiru na kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC

Jihar Kaduna - A yau ake shirin yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Kaduna kamar yadda aka yi a sauran jihohi.

Kamar jihar Kano, kotun da ke Kaduna ta yanke shawarar gabatar da shari'ar ta manhajar 'Zoom'.

Kotun zabe a Kaduna za ta yanke hukunci ta manhajar 'Zoom'
Kotun Kararrakin Zabe A Jihar Kaduna Ta Fara Yanke Hukunci. Hoto: Uba Sani.
Asali: Facebook

Yaushe ake shari'a tsakanin Uba Sani da Isa Ashiru a Kaduna?

Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Isa Ashiru na kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC da aka gudanar a watan Maris, Daily Trust ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Bukatar Gwamna Sani a Kan Karar PDP Da Ashiru

Kotun ta samar da kayayyaki don tabbatar da gudanar da shari'ar ta 'Zoom' a cikin kotun.

Har zuwa karfe 9:50 na safe ba a fara gudanar da shari'ar ba saboda shirye-shirye da ake a kotun.

Har ila yau, an jibge jami'an tsaro a harabar kotun da ke Kawo a cikin Kaduna, cewar The Nation.

Wane kara kotun ta fara kora a Kaduna?

Yayin yanke hukuncin da ake yi yanzu, kotun ta yi fatali da karar Gwamna Uba Sani na APC fa ya shigar kan Isa Ashiru na jam'iyyar PDP.

Sani na tuhumar jam'iyyar PDP ne da cewa ta shigar da kara bayan kwanaki 21 da kotun ta ba su dama.

Sai dai mai Shari'a, Victor Oviawe ya tabbatar da cewa an shigar da karar a lokacin da ya dace.

Kotu ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir a na Kano

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Kano ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP saboda kura-kurai.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

Kotun har ila yau, ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar.

Tun farko Nasiru Gawuna na kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Maris inda ya ce akwai kura-kurai sosai a zaben da ya bai wa Abba Kabir nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel