Yan Daba Sun Farmaki Jigon SDP a Jihar Kogi, Sun Banka Wa Motarsa Wuta

Yan Daba Sun Farmaki Jigon SDP a Jihar Kogi, Sun Banka Wa Motarsa Wuta

  • Tsagerun 'yan daba sun kai hari gidan wani jigon jam'iyyar SDP a jihar Kogi yayin da ake tunkarar zaben gwamna a watan Nuwamba
  • Maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wani kana suka ƙona motocin da suka taras a gidan
  • Daraktan yakin neman zaben SDP ya kai ziyara wurin, inda ya yi Allah wadai da abin da maharan suka aikata

Jihar Kogi - Wasu ‘yan daba sun kai farmaki gidan wani jigo a jam’iyyar SDP, Abdul Yusuf Amichi, wanda aka fi sani da Abdul limbo, da ke Ugwolawo, karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa yayin wannan harin 'yan daban sun banka wa motar ɗan siyasan wuta a gidansa.

Yadda aka kai hari gidan ɗan SDP.
Yan Daba Sun Farmaki Jigon SDP a Jihar Kogi, Sun Banka Wa Motarsa Wuta Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A cewar shaidu, maharan waɗanda suka kutsa cikin gidan da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba sun yi ta tafka aika-aika har zuwa safiyar Alhamis.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Koma Jami'ar Gwamnatin Tarayya, Sun Sace Ma'aikata

"Sun kona motar yakin neman zaben SDP tare da lalata gidan wani mai goyon bayan SDP, Abdul Yusuf Amichi da ke gunduma ta 1 a yankin Ugwolawo."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Haka nan sun buɗe wuta da bindigogi a gidan Abdul Limbo da ke Ugwolawo gunduma ta 1, sun lalata gidan gaba ɗaya," in ji wani mazaunin yankin, Abu Alijenu.

Jigon SDP ya bayyana yadda lamarin ya faru

A cewar ɗan siyasan da harin ya shafa, 'yan bindiga sun kutsa kai cikin gidansa da daddare kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Garin haka ne suka bankawa motar kamfen jam'iyyar SDP wuta, suka yi kaca-kaca da motar Mista Limbo, kana daga bisani suka yi awon gaba kayayyaki masu daraja.

"Na kai rahoton abin da ya faru ga 'yan sanda," in ji Jigon LP, wanda aka kai hari gidansa, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

Darakta Janar na yakin neman zaben SDP, Sheik Ibrahim Jibrin, wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya yi Allah wadai da harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa kiran da aka yi masa ba ko sakon waya.

Oyo: Shugabar Matan APC Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Sanata Ya Yi Ta'aziyya

A wani rahoton kuma Allah ya yi wa shugabar matan jam'iyyar APC ta mazaɓar jihar Oyo ta arewa, Princess Adebowale Atoyebi rasuwa.

Sanatan Oyo ta kudu, Sharafadeen Alli, ya yi ta'aziyyar wannan rashi ga iyalai da ɗaukacin mutanen jihar Oyo da APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel