Gwamnan Zamfara Ya Ba da Umarnin ‘da Gani a Sheke’ Kan Masu Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba

Gwamnan Zamfara Ya Ba da Umarnin ‘da Gani a Sheke’ Kan Masu Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba

  • Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana sanya dokar haramta hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar baki daya
  • Ya kuma umarci jami’an tsaro su sheke duk wanda suka gani yana hakar ma’adinai ba tare da umarnin gwamnati ba
  • Ana yawan samun ayyukan ta’addanci da barna r’yan bindiga a yankunan jihar Zamfara, hakan na jawo asarar rayuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gusau, jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kawo dokar hana hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba a jihar a ranar Asabar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya kuma umurci jami'an tsaro da su bindige duk wadanda suka karya dokar da zarar an ga suna hakar ma’adinai a jihar.

Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Malam Suleiman Idris, ya bayyana cewa, Lawal ya fadi haka ne a Gusau, inda ya ce wannan umarni na daga cikin matakan dawo da doka da oda a jihar.

Kara karanta wannan

Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a

An haramta hakar ma'adinai a Zamfara
An hana hakar ma'adinai a Zamfara | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Abin da yasa aka saka dokar

Gwamnan ya lura cewa, hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ya haifar da karuwar ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka a sassan Zamfara na tsawon shekaru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Babu shakka, hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba na daya daga cikin abubuwan da suka ta’azzara barnar ’yan bindigar da suka addabi Zamfara.
"Dole ne mu dauki matakin gaggawa don dakile wannan matsala da kuma maido da zaman lafiya da tsaro a cikin al'ummominmu."

Abin da gwamna yake so daga hukumomin tsaro

Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su dauki tsauraran matakai kan wadanda aka kama suna karya dokar, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, lokaci ya yi da za a kawo karshen ayyukan ta’addanci da barnar ganganci da kuma aiwatar da matakan kare lafiya da jin dadin jama’a.

Gwamnan ya ce:

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Malaman jami'a sun ci taliyar karshe saboda aikata badala da rashawa

“Wannan umarni ya zama dole domin tabbatar da tsaro da lafiyar al’ummar Zamfara da kuma dakile masu aikata laifuka.
“Haka kuma wani mataki ne na gaggawa don baiwa gwamnati damar kula da dukiyar ‘yan jihar baki daya tare da toshe ayyukan da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.”

Mutane sun mutu wajen hakar ma’adinai

A wani labarin, mutane uku sun mutu bayan da wata mahakar ma'adanai da suke aiki a ciki ta rufta a yankin Anyiin da ke karamar hukumar Logo a jihar Benue, ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa marigayan sun kasance suna cikin hako ne lokacin da ramin ya rufta dasu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mamatan sun mutu nan take yayin da mutanen gari kuwa suka yi kokarin ceto wadanda suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.