Leah Sharibu Ta Zama Likitar Da Ke Kula Da Mayakan ISWAP A Jihar Borno

Leah Sharibu Ta Zama Likitar Da Ke Kula Da Mayakan ISWAP A Jihar Borno

  • Mayakan ISWAP na ci gaba da rike wadanda su ka kama don taimakonsu ta bangarori da dama yayin da su ke cikin yaki
  • Daya daga cikinsu, Leah Sharibu wacce ke hannun mayakan tun 2018 ta na jagorantar tawagar ba da daukin gaggawa
  • An sace Sharibu ne tare da sauran dalibai 109 daga Kwalejin Makarantar Mata ta Gwamnati da ke Dapchi a jihar Yobe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno – Daya daga cikin ‘yan matan Dapchi da ke hannun ‘yan kungiyar ISWAP, Leah Sharibu ta dawo ma’akaciyar jinya.

Sharibu yanzu ita ke jagorantar masu ba da kulawar gaggawa ga mayakan ISWAP da su ka samu rauni a yayin gumurzu.

Sharibu na jagorantar tawagar kula da lafiya na mayakan ISWAP
Sharibu Ta Zama Likitar Da Ke Kula Da Mayakan ISWAP. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Yaushe aka sace Sharibu a Borno?

An sace Sharibu ne tare da sauran dalibai 109 daga Kwalejin Makarantar Mata ta Gwamnati da ke Dapchi a jihar Yobe a ranar 19 ga watan Faburairu na 2018.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe mata biyar daga cikin daliban yayin da Kungiyar ISWAP ta dawo da guda 104 ga iyalansu amma ban da Sharibu.

An ruwaito cewa kungiyar ta ci gaba da rike Sharibu ne saboda ta ki bin umarnin kungiyar da kuma Musulunta.

Wane hali Sharibu ta ke ciki?

Daily Trust ta tataro cewa an bai wa Sharibu horo na musamman a kan jinya da kula da lafiya wanda ta ke kula da marasa lafiya na mayakan Boko Haram.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar cewa mayakan na tilasta horas da wadanda su ka kama ta bangaren jinya da kere-kere da fannin na’ura mai kwakwalwa da sauransu.

Majiyar ta ce:

An bai wa Sharibu horo na musamman a bangaren jinya kuma yanzu haka ita ke jagorantar tawagar kawo dauki idan an samu rashin lafiya na mayakan ISWAP a yankin Tafkin Chadi.”

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

Sharibu ta sake aurar wani daga cikin kwamandojin yakin bayan rabuwa da mijinta na farko da ta haifa wa yara biyu, Politics Nigeria ta tattaro.

Sharibu ta haifi jariri a hannun mayakan Boko Haram

A wani labarin, Leah Sharibu da ke hannun mayakan Boko Haram na tsawon lokaci ta dauki ciki har ta haifi yaronta namiji.

Sharibu na daga cikin 'yan matan da aka sace makarantar Dapchi da ke jihar Yobe a shekarar 2018 wanda da dama daga cikinsu mayakan sun sake su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel