Abun Bakin Ciki
Jami'an yan sandan Lagas sun kama dan yaho mai shekaru 32, Afeez Olalere wanda ya kashe kaninsa domin yin kudin asiri bayan boka ya nemi ya kawo sassan jikinsa.
Jami'an rundunar yan sandan jihar Nasarawa sun damke wani mutum mai shekara 43, Dan'asabe Eddo bisa zarginsa da kwantawa da tsohuwa yar shekara 80 a jihar.
Tsohon Atoni Janar na jihar Kaduna, Barista Rabo Barde, ya mutu. Ya mutu a ranar Litinin 3 ga watan Janairu yayin da yake farfadowa daga wata rashin lafiya.
Wani matashi mai shekaru 21, Auwal Abdulrasheed ya shiga hannun yan sanda a jihar Kano bayan ya yi garkuwa da budurwa tare da yankata da kuma neman kudin fansa.
Rahoton da muka samu daga jihar Bayelsa ya nuna cewa wata yar gaddama ta yi sanadiyyar kashe wani ɗan okada a yankin Sagbama dake jihar da safiyar yau Alhamis.
Mahaifin Farouk Abdul Mutallab, wanda aka yankewa hukuncin daurin rai-da-rai a kasar Amurka saboda ta'addanci, ya ce yana fatan sake ganin dan nasa a rayuwarsa.
Wani abun bakin ciki ya ya afku a jajiberin sabuwar shekara lokacin da wasu matasa biyu yan gida daya suka nitse a kogin Asa da ke Kwara a yayin da suke wanka.
Al'umman Ogbinbiri da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa sun shiga alhini a jajiberin sabuwar shekara sakamakon mutuwar wani fasto da mutum shida.
Mutum 7 ciki harda magidanci da matansa ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a kauyen Zhigiri a karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.
Abun Bakin Ciki
Samu kari