Gwamna Radda na Ganin Ƙiyayya, an Ƙona Motoci a Tawagar Kamfen Dinsa
- Wasu ’yan daba sun kai hari a garin Yankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a Katsina, inda suka ƙona motoci biyu
- Harin ya faru ne yayin da magoya bayan APC da jami’an gwamnati ke jiran isowar Gwamna Dikko Radda domin halartar gangamin siyasa
- Ƙungiyar Musa Adamu Network ta yi Allah wadai da harin, tare da buƙatar jami’an tsaro su gudanar da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari tare da ƙona motoci biyu, ciki har da motar ƙungiyar siyasa ta Musa Adamu Network (MAN).
Lamarin ya faru ne a garin Yankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a Katsina, inda mutane da dama suka jikkata, wasu shaguna kuma suka lalace.

Source: Original
An sake kona motocin APC a Katsina
Hakan ya zo ne yayin shirye-shiryen tarbar Gwamna Dikko Umaru Radda a wani gangamin siyasa, lokacin da magoya baya da jami’an yankin ke jiran isowarsa fadar mai martaba, cewar Punch.
Shugaban kwamitin shugabannin ƙungiyar MAN, Alhaji Nura Sule Yandaki, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa Faskari domin halartar gangamin siyasar gwamnan lokacin da aka kai harin.
A cewarsa, an samu tashin hankali a Yankara bayan rahotannin gudanar da jerin gwanon Mauludi da wata ƙungiyar addinin Musulunci ta yi, inda ake zargin wasu ’yan daba sun yi amfani da lamarin wajen kai wa motocin da ke wucewa hari.
Yandaki ya bayyana cewa yana tare da mambobin ƙungiyar guda 11 waɗanda aka zaɓa domin halartar gangamin, inda ya ƙara da cewa duk sun tsira ba tare da sun samu rauni ba, duk da lalata motarsu.
Wani jami’in ƙaramar hukumar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutane da dama sun samu raunuka, yayin da aka lalata motoci biyu tare da cinna musu wuta.
Jami’in ya kuma bayyana cewa wasu shaguna sun lalace sakamakon rikicin, sai dai ba a iya tantance yawan barnar da kuma adadin waɗanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata ba.
Ya bayyana cewa tashin hankalin ya ɓarke ne yayin da mazauna yankin, magoya bayan siyasa da jami’an gwamnati ke jiran isowar gwamnan fadar mai martaba.
Sai dai jami’in ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun dawo da zaman lafiya, kuma harkokin yau da kullum sun koma yadda suke a garin.
Ya ce:
“Yanzu komai ya daidaita. Lamarin ya faru ne lokacin da muke jiran tarbar gwamna a fadar mai martaba, amma tun daga lokacin komai ya koma daidai.”

Source: Facebook
Yadda aka kona motar APC a Katsina
Har ila yau, a wani bidiyo da Leadership ta yada, ya nuna wasu matasa suna kai wa mota hari kafin daga bisani su cinna mata wuta.
Wani bidiyon kuma ya nuna wani jami’in tsaro da alama ya samu munanan raunuka, yana karɓar magani a kan gadon asibiti, tare da alamun jini a jikinsa.
Sai dai ba a iya tabbatar da sunan jami’in tsaron da ya jikkata, girman raunukansa ko kuma ainihin yanayin da aka ɗauki bidiyon ba kafin kammala wannan rahoto.
Da yake mayar da martani kan lamarin, sakataren ƙungiyar MAN Network, Alhaji Shamsuddeen Sani Lema, ya yi Allah wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin dabbanci da abin da ba za a amince da shi ba a tsarin dimokuraɗiyya.
Lema ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan rikicin, gano waɗanda ke da hannu tare da hukunta su bisa doka.
Gwamna Radda ya nemi alfarmar Katsinawa
An ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, na ci gaba da ziyarar yankunan jihar Katsina yayin da yake yakin neman zabe.
Ziyarar ta sa ta kai shi karamar hukumar Dandume inda ya gana da masu ruwa da tsaki da magajin Dandume.
A yayin ziyarar, Katukan Katsina kuma Hakimin Dandume, ya yaba wa Gwamna Radda kan alkawuran da ya cika.
Asali: Legit.ng


