Babbar Matsala Ta Tunkaro Tinubu, Rikicin Tikitin Sanatan APC Zai Iya Taɓa Ƙuri'unsa

Babbar Matsala Ta Tunkaro Tinubu, Rikicin Tikitin Sanatan APC Zai Iya Taɓa Ƙuri'unsa

  • Kungiyar Renewed Hope Foot Soldiers for Tinubu ta yi gargadin cewa rikicin tikitin sanatan Imo West na iya jawo wa APC koma baya a Kudu maso Gabas
  • Kungiyar ta ce hukuncin kotun tarayya da ya amince da Rochas Okorocha a matsayin dan takarar APC na iya kara rikicin siyasa a Imo
  • Ta bukaci shugabancin APC ya tabbatar da adalci da gaskiya, tana mai cewa nuna wa Gwamna Hope Uzodinma wariya na iya shafar nasarar Tinubu a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wata kungiyar siyasa mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta yi gargadi kan tikitin sanata a Imo.

Ta ce rikicin tikitin sanatan Imo ta Yamma na APC na iya jawo koma baya tare da kawo cikas ga burin Tinubu na sake lashe zabe a 2027.

Kara karanta wannan

Akwai babban dalili: Makiyaya sun faɗi musabbabin shirin goyon bayan Tinubu

Ana ganin Tinubu zai samu matsala saboda tikitin sanatan Imo
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Kungiyar ta ce hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, wanda ya amince da tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, a matsayin halastaccen dan takarar, cewar Vanguard

Ta ce hakan na iya kara ruruta rikicin siyasa a yankin, tare da kawo cikas ga kokarin tabbatar da hadin kan jam'iyyar gabanin babban zabe mai zuwa.

Kungiyar na kasa, Hon. Gbenga Owojori, ya sanya wa hannu, kungiyar ta nuna damuwa kan yadda rikicin zai iya shafar muradun siyasa na Gwamna Hope Uzodinma, musamman rahotannin da ke cewa yana sha'awar zama shugaban majalisar dattawa ta 11.

Uzodinma, wanda ya taba zama sanata, na daga cikin wadanda magoya bayansa ke ganin sun cancanci kujerar, inda kungiyar ta yi ikirarin cewa manyan 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban suna goyon bayan takararsa.

Ta bayyana cewa rikicin tikitin Imo ta Yamma ya wuce batun mazabar kawai, musamman ganin yadda ake fara bayyana dabarun siyasa da suka shafi wanda zai jagoranci majalisar dattawa ta 11.

Kara karanta wannan

Jerin labaran karya da suke yawo a yanar gizo da za a iya dauka gaskiya ne

Kungiyar ta ce:

"Rikicin tikitin Imo West yana da sakamako da ya wuce mazabar. Ya sauya lissafin siyasar da ta shafi shugabancin majalisar dattawa, tare da haifar da fargabar cewa za a iya hana wani babban dan takara daga Kudu maso Gabas shiga takarar kafin a kafa sabuwar majalisar."

Kungiyar ta kuma yi magana kan zarge-zargen da wasu masu suka ke yi cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, na iya kasancewa yana da muradin hana Uzodinma zama abokin hamayyarsa a takarar shugabancin majalisar dattawa.

Ta kuma ambaci ikirarin da ake dangantawa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan kokarin shigar da karar kalubalantar gwamnan Imo a kotu.

A cewar kungiyar, masu suka sun danganta wadannan zarge-zarge da goyon bayan da Akpabio ya taba bai wa Wike a lokacin rikicinsa da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.

Okorocha ya caccaki Gwamna Uzodinma

Kun ji cewa tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya ce Sanata Hope Uzodinma bai taɓa lashe zaɓe ba a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya sake taso Bola Tinubu a gaba, ya fadi shirmen da ya yi

Ya yi wannan furuci ne bayan kotu ta soke nasarar Uzodinma a zaɓen fitar da gwani na APC na takarar sanata.

Okorocha ya ce shi ne ya lashe tsaida fidda gwani, kuma tun can da magudi gwamnan Imo yake cin takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.