Innalillahi: Ubangiji Ya Karbi Rayuwar Mai Kula da Daki da Kabarin Manzon Allah, SAW

Innalillahi: Ubangiji Ya Karbi Rayuwar Mai Kula da Daki da Kabarin Manzon Allah, SAW

  • Allah ya karbi rayuwar daya daya cikin masu hidima ga masallacin Manzon Allah (SAW) da ke birnin Madina na kasar Saudiyya
  • Marigayin Abdou Idris Ali ya rasu a jiya Litinin 20 ga watan Nuwamba wanda ya dade ya na hidimar gadin kabarin Manzon Allah
  • An gudanar da sallar jana'izarsa a jiyan kamar yadda tsarin addinin Musulunci ya tanadar tare da kai shi makwancinshi na karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Madina, Saudiyya - Mai kula da kabarin Manzon Allah (SAW), Abdou Ali Idris ya riga mu gidan gaskiya, Islamic Information ta tattaro.

Sheikh Abdou Ali kafin rasuwarshi shi ne kuma ke kula da dakin Manzon Allah (SAW) wanda ya dade ya na hidima ga masallacin Madina.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Manjo Janar Chris Alli rasuwa

Mai gadin kabarin Manzon Allah, SAW ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin ya rasu a jiya Litinin a Madina. Hoto: @theholymosques.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin, Abdou ya rasu a Madina?

Hukumar masallatan Harami sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a jiya Litinin 20 ga watan Nuwamba a birnin Madina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni aka yi sallar jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a masallacin Manzon Allah, Amininya ta tattaro.

An gudanar da sallar jana'izarshi bayan sallan mangariba yayin da dubban mutane su ka halarta tare da masa addu'o'in samun rahama.

Mutane nawa su ka rasa rayukansu a yayin aikin?

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin shi ne na uku da ya rasu cikin shekaru 10 da su ka gabata cikin masu hidima ga masallacin.

Majiyar ta tabbatar cewa a baya masu aikin sun haura mutum duba daya amma daga baya wadanda su ka rage a raye yanzu ba su wuce mutane biyar ba.

Kara karanta wannan

Rahoto ya hango tsananin tashin farashin kayayyakin abinci a shekarar 2024, ga dalilin da ya ja

Marigayin ya ba gudunmawa mai tarin yawa a kokarin kula da kabarin wanda za a shafe shekaru ba tare da an manta da shi ba.

Babban malamin Musulunci, Imam Sa'idu ya rasu

A wani labarin, Shahararren malamin addinin Musulunci, Imam Sa'idu Abubakar ya riga mu gidan gaskiya a Gombe.

Marigayin kafin rasuwarshi shi ne babban limamin masallacin Izala da ke Abuja Low Cost.

Gwamna Muhammad Inuwa na jihar Gombe ya mika sakon ta'aziya inda ya bayyana rashin a matsayin babban gibi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel