Innalillahi: Mummunan Hatsarin Tirela Ya Yi Ajalin Mutane 17, Fiye da 200 Sun Jikkata a Neja

Innalillahi: Mummunan Hatsarin Tirela Ya Yi Ajalin Mutane 17, Fiye da 200 Sun Jikkata a Neja

  • An rasa rayuka da dama bayan wani mummunan hatsarin mota da ya yi ajalin mutane 17 da jikkata fiye da 200 a jihar Neja
  • Hatsarin ya afku ne a jiya Talata 21 ga watan Nuwamba da misalin karfe 3 na yamma a kauyen Takalafiya da ke jihar
  • Kakakin hukumar FRSC, Bisi Kazeem shi ya bayyana haka a yau Laraba 22 ga watan Nuwamba inda ya ce an kwashi gawarwakin zuwa asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja - Wani mummunan hatsarin motar tirela ya yi ajalin mutane akalla 17 tare da jikkata wasu a jihar Neja.

Hatsarin ya afku ne a kauyen Takalafiya da ke karamar hukumar Magama da ke jihar, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa wani hukuncin kisa kan kashe jami’an DSS 7 a shekarar 2015

Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 17, fiye da 200 sun samu raunuka
Hatsarin mota ya yi ajalin mutane 17 a Neja. Hoto: FRSC.
Asali: Facebook

Mutane nawa su ka rasa rayukansu a hatsarin?

Hukumar FRSC ita ta bayyana haka a yau Laraba 22 ga watan Nuwamba a Minna babban birnin jihar, Ripples ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar, Bisi Kazeem ya ce akalla mutane 229 sun jikkata wanda ya hada da yara mata hudu da maza biyar.

Ya ce:

"A cikin mutane fiye da 200 da hatsarin ya rutsa da su, an ceto wasu dama da raunuka yayin da manyan maza guda 17 su ka mutu."

Kazeem ya ce hatsarin ya afku yayin da wani direban babban motar tirela mai suna Ido Doba ya gagara shawo kan motar.

An kwashi gawarwakin zuwa asibiti

Wadanda su ka samu raunaka a hatsarin an kwashe su zuwa babban asibitin Kontagora, cewar Daily Post.

Yayin da aka kwashi gawarwakin zuwa inda ake adana gawarwaki na asibitin da ke Kontagora.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki gidan kakakin majalisa, ana zargin jami'an tsaro da hannu a harin

Hukumar har ila yau, ta gargadi direbobi da su guji kwasar jama'a a cikin motocinsu saboda hakan barazana ce ga rayukan fasinjoji da mutane a kan hanya.

Hatsarin mota ya yi ajalin mutane 4 a jihar Kano

A wani labarin, wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane akalla 4 a kauyen Dinyar Madiga a jihar Kano.

Hatsarin ya afku ne a ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba a kauyen Dinyar Madiga da ke karamar hukumar Takai inda mutane da dama suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel