2027: INEC Ta Mayar da Sunan Pantami, an Hango Abin da Hakan Zai Jawo ga Mutanen Gombe

2027: INEC Ta Mayar da Sunan Pantami, an Hango Abin da Hakan Zai Jawo ga Mutanen Gombe

  • PDP reshen Gombe ta yaba wa INEC bisa ɗora sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a shafinta, bayan hukumar ta tabbatar ya cika sharuddan takarar gwamna
  • Jam’iyyar ta ce amincewa da Pantami za ta faɗaɗa damar zaɓin masu kaɗa ƙuri’a, tare da inganta gasa da siyasa mai ma’ana a jihar
  • PDP ta musanta rahoton cewa shugabanninta na ƙananan hukumomin Kwami da Nafada sun sauya sheka zuwa APC, tana mai cewa har yanzu mambobinta ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa ɗora sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a shafinta na intanet.

Pantami, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Majidadin Daular Usmaniyya, ya samu amincewar INEC domin shiga takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gano hanyar da Tinubu zai samu kuri'u cikin sauki a 2027

An dawo da sunan Pantami cikin 'yan takara
Farfesa Isa Ali Pantami na addua a wajen taro Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamban 2026, PDP ta bayyana matakin a matsayin wani babban ci gaba ga dimokuraɗiyya, shigar kowa cikin harkokin siyasa da kuma mutunta haƙƙin ’yan Najeriya na tsayawa takara.

Me PDP ta ce kan amincewa da Pantami?

PDP ta bayyana cewa amincewa da takarar Pantami za ta ƙara wa siyasar Gombe armashi, tare da bunƙasa gasa tsakanin ’yan takara.

Jam’iyyar ta ce hakan zai bai wa masu kaɗa ƙuri’a damar samun zaɓi mai faɗi, domin su tantance ’yan takara bisa manufofinsu da irin shugabancin da suke son samu.

Haka kuma, PDP ta gode wa magoya bayanta da suka bayar da gudummawa ta hanyar addu’o’i, shawarwari da goyon baya a tsawon lokacin da ake gudanar da tantance cancantar Pantami.

Ta buƙaci ’yan siyasa a jihar da su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen ci gaba, tare da gudanar da kamfen cikin lumana da mutunta juna.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya fito da abin da ya kamata mutane su sani kan takarar Pantami da Aminu Gwarzo

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga INEC da ta ci gaba da kasancewa mai zaman kanta, tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

A cewar PDP:

“Al’ummar jihar Gombe sun cancanci sahihin tsarin zaɓe, inda ƙuri’unsu za su yi tasiri, kuma a mutunta muradun da suka bayyana baki ɗaya.”

PDP ta musanta sauya shekar shugabanninta

A wani labarin kuma, PDP reshen Gombe ta musanta zargin cewa shugabanninta na ƙananan hukumomin Kwami da Nafada sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Jam’iyyar ta mayar da martani ne kan ikirarin da wani jigon APC ya yi yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a matakin jiha. An gudanar da bikin ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa da ke birnin Gombe.

A cikin sanarwar da ta fitar, PDP ta ce zargin ba gaskiya ba ne, tana mai jaddada cewa shugabannin ƙananan hukumomin biyu har yanzu cikakkun mambobinta ne. Jam’iyyar ta kuma ce babu ɗayansu da ya taɓa nuna sha’awar komawa APC.

PDP ta zargi APC da yaɗa farfaganda

PDP ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda ta ce wani babban jigo da ya taɓa riƙe muƙami a matakin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ya yaɗa bayanin da ba gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, INEC ta amince da takarar Sheikh Pantami da Aminu Gwarzo a zaɓen 2027

Jam’iyyar ta gargaɗi APC mai mulki da ta daina yaɗa bayanan ƙarya game da mambobinta da jami’anta.

Ta zargi jam’iyyar mai mulki da amfani da farfaganda domin neman samun goyon bayan jama’a, maimakon mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi al’ummar jihar.

Pantami ya dawo cikin 'yan takara
Farfesa Isa Ali Pantami na jawabi a wajen taro Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Abokin hamayyar Pantami ya aiko da sako

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Gombe, Jamilu Gwamna ya bayyana cewa ba zai lamunci rashin hada kan jama'a ba.

Ya bayyana cewa dole duk wanda yake so a dama da shi a gwamnatin shi ya dage da neman jama'a ta yadda zai iya kawo akwatinsa a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng