Jimami Yayin da Aka Tsinci Gawar Lakcara a Cikin Ofishinsa Na Jami’a, an Bayyana Halayensa

Jimami Yayin da Aka Tsinci Gawar Lakcara a Cikin Ofishinsa Na Jami’a, an Bayyana Halayensa

  • Ana cikin jimami bayan mutuwar wani lakcara a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun a jiya Talata
  • Marigayin mai suna Dakta Ayo Ojediran ya rasu da yammacin jiya Talata bayan an tsinci gawarshi a cikin ofishinsa
  • Lakcaran wanda ke koyarwa a tsangayar Kimiyya da Fasaha a Jami’ar an bayyana shi da mutumin kirki kuma mai taimako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun – An shiga wani irin yanayi bayan tsintar gawar lakcara a Jami’ar Obafemi Awolowo, OAU da ke jihar Osun.

Marigayin mai suna Dakta Ayo Ojediran na tsangayar Kimiyya da Fasaha na Jami’ar kafin rasuwarshi, Vanguard ta tattaro.

Lakcaran Jami'ar OAU ya riga mu gidan gaskiya a cikin ofishinsa
Lakcaran ya mutu ne a cikin ofishinsa da ke Jami'ar. Hoto: OAU.
Asali: UGC

Yaushe lakcaran ya rasu a Jami’ar OAU?

Kara karanta wannan

Innalillahi, Wani babban Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Rahotanni sun tattaro cewa abokan aikin lakcaran ne suka tsinci gawar a jiya Talata 14 ga watan Nuwamba a cikin ofishinsa, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin abokan aikin nasa sun bayyana mutuwar Ayo a matsayin abin takaici da kuma bakin ciki inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

Wani daga cikin ‘yan uwan mamacin, Ayodeji Obisesan ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa marigayin a kullum kokarin taimako ya ke.

Mene martanin mutane kan mutuwar lakcaran OAU?

Ya ce:

“Wannan mutumin kirki ne ba shi da matsala ko kadan, a kullum burinsa ya zai yi ya taimaki jama’a.
“Ubangiji ya bai wa dalibanka da abokan arziki da kuma ‘yan uwanka hakurin jure wannan babban rashi.”

Kakakin Jami’ar ta OAU, Abiodun Olarewaju ya tabbtar da faruwa lamarin inda ya ce sun ji mutuwar sosai a jikinsu, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

Matashin mawaki ‘Oladips’ ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, matashin mawaki mai suna Oladipopu Oladimeji Olabode ya riga mu gidan gaskiya a daren jiya Talata 14 ga watan Nuwamba a Legas.

Marigayin wanda aka fi sani da ‘Oladips’ ya rasu ya na da shekaru 28 kacal a duniya bayan fama da jinya mai tsayi.

Wannan na zuwa ne watanni biyu da mutuwar matashi 'Mohbad' mai sheakru 27 a Legas da ta jawo cece-kuce a fadin Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel