Yadda Matashi Dan Shekaru 20 Ya Kashe Mahaifinsa a Kaduna

Yadda Matashi Dan Shekaru 20 Ya Kashe Mahaifinsa a Kaduna

  • Wani matashi dan shekaru 20, da ya kashe mahaifinsa ya shiga hannu a jihar Kaduna
  • David Felix wanda ya fito daga kauyen Madakiya, a karamar hukumar Zango-Kataf ya make mahaifin nasa da muciya har lahira
  • Ya yi zargin cewa mahaifin na zuwa masa a matsayin tsuntsu mai fuskar mutum a cikin mafarkinsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wani matashi dan shekaru 20, David Felix, ya kashe mahaifinsa kan cewa yana zuwa masa a cikin mafarki.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, matashin ya aikata laifin ne a gidansu da ke kauyen Madakiya, karamar hukumar Zango-Kataf ta jihar Kaduna.

Matashi ya sheke mahaifinsa a Kaduna
Yadda Matashi Dan Shekaru 20 Ya Kashe Mahaifinsa a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda matashi ya sheke mahaifinsa a Kaduna saboda mafarki da shi

Kara karanta wannan

Dan caca da ya ciyo N102m zai taimakawa dalibin da yayi asarar kudin karatunsa a caca

An tattaro cewa Felix ya yi zargin cewa mahaifinsa na zuwa masa a mafarki a matsayin tsuntsu mai dauke da fuskar mutum, yana kokarin cutar da shi, saboda haka bai da wani zabi da ya wuce ya kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda yan sanda suka rahoto, lamarin ya afku ne a ranar 30 ga watan Satumba, kafin aka kama yaron,

An tattaro cewa yayin da ake yi masa tambayoyi a hedkwatar rundunar yan sanda, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, yana mai nuna nadama kan abun da ya aikata.

Ya bayyana yadda ya dauki matakin bayan ya tashi daga bacci, inda ya yi amfani da tabarya wajen sheke mahaifinsa yayin da yake tsaka da bacci.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, wanda ya gabatar da mai laifin ga manema labarai a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, ya sanar da cewar za a gurfanar da shi da zaran an kammala bincike.

Kara karanta wannan

‘Dan wasan fim zai mikawa Gwamna Abba rikon yaransa 2 saboda dakatar da shi

Jaridar Vanguard ta nakalto ASP Hassan yana cewa:

"Ya kashe mahaifinsa bayan ya farka daga bacci kuma ya yi amfani da tabarya wajen bugunsa yayin da yake bacci. Za a shigar da tuhume-tuhume a kansa da zarar an kammala bincike."

An kama matashi kan ba budurwa guba

A wani labarin, mun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani dalibin shekarar karshe a jami’ar aikin gona ta tarayya da ke Abeokuta, mai suna Oladokun Ayomide.

Rundunar ta kama Ayomide bisa zarginsa da kashe budurwarsa mai suna Ugbokwe Mmasichukwu da wata mata mai suna Odumosu Semilore.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel