Dogara Ya Kare Tinubu kan Rashin Tsaro, Ya Fadi Lokacin da Matsalar Ta Fara a Najeriya

Dogara Ya Kare Tinubu kan Rashin Tsaro, Ya Fadi Lokacin da Matsalar Ta Fara a Najeriya

  • Yakubu Dogara ya ce ta'addanci, 'yan bindiga, garkuwa da mutane da rikicin al'umma sun dade a Najeriya tun kafin Tinubu ya zama shugaban kasa
  • Dogara ya danganta matsalolin tsaron da rashin tsaron iyakokin kasa, yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba, rashin aikin yi da akidun tsattsauran ra'ayi
  • Shugaban Jami'ar Achievers ya bayyana damuwarsa kan makomar daliban da suka kammala karatu, duk da karuwar jami'o'i a Najeriya zuwa 312

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ondo - Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya bayyana cewa matsalolin tsaron da Najeriya ke fama da su sun samo asali ne tun kafin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki.

Dogara ya ce ta'addanci, tada kayar baya da ayyukan 'yan bindiga sun dade suna addabar kasar tun kafin shekarar 2023, lokacin da Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Dan Atiku ya faɗi dalilin fanɗarewa ubansa, ya ɗauki alƙawari ga Tinubu

Dogara ya kare Shugaba Tinubu
Yakubu Dogara da shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tsohon shugaban majalisar, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na jami'ar Achievers University da ke Owo, jihar Ondo, ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye dalibai karo na 16 na jami'ar, cewar rahoton Daily Trust.

A yayin bikin, dalibai 836 ne suka samu shaidar kammala karatu a matakai daban-daban.

Dogara ya fadi tushen matsalar tsaron Najeriya

Dogara ya ce matsalolin tsaron kasar sun samo asali ne daga abubuwa da dama da suka dade suna faruwa, ciki har da rashin tsaron iyakokin kasa, yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma rashin aikin yi tsakanin matasa.

Ya kuma danganta matsalolin da yaduwar akidun tsattsauran ra'ayi, wadanda suka taimaka wajen kara ta'azzara matsalar tsaro a sassa daban-daban na kasar.

A cewarsa, bai kamata a danganta fara matsalar rashin tsaro da gwamnatin Tinubu ba, domin lamarin ya dade yana faruwa tun kafin hawansa mulki a watan Mayun 2023, The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Ruɗani: INEC ta ɗora NDC amma babu sunan Aminu Gwarzo a jerin 'yan takarar gwamnan Kano

"Matsalar rashin tsaro a Najeriya ba ta fara da wannan gwamnati ba. Wannan ba yana nufin muna kare wani ba ne, domin hujjojin da ake da su ba sa bukatar kariya. Ta'addanci, tada kayar baya, ayyukan 'yan bindiga, garkuwa da mutane da rikicin al'umma ba su zo Najeriya a shekarar 2023 ba." In ji shi.

Ya kara da cewa wadannan matsaloli sun samo asali ne daga abubuwan da suka faru tsawon shekaru masu yawa.

Dogara ya yi magana kan kokarin Tinubu

Duk da bayyana cewa matsalolin tsaro sun riga sun wanzu kafin zuwan gwamnatin yanzu, Dogara ya ce Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa samar da tsaro na daga cikin manyan nauyin da gwamnatinsa ta dauka.

Ya jaddada cewa kalaman nasa ba wai don kare gazawar wata gwamnati ba ne, sai dai domin bayyana hakikanin tarihin matsalar tsaron Najeriya.

Haka kuma, ya taya daliban da suka kammala karatu murna, yana mai cewa Najeriya na matukar bukatar basirarsu, kirkire-kirkirensu da sabbin dabarun da za su taimaka wajen ci gaban kasa.

Shugaban jami'a ya nuna damuwa kan makomar dalibai

A nasa jawabin, Pro-Chancellor na jami'ar Achievers, Farfesa Bode Ayorinde, ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen fadada damar samun ilimin jami'a.

Sai dai ya nuna damuwa kan irin damar da ke jiran daliban da suka kammala karatu bayan barin makarantu, musamman wajen samun ayyukan yi da amfani da ilimin da suka samu.

Kara karanta wannan

An yi wa Shehin malamin Musulunci rashin kunya a masallaci saboda Tinubu

Ayorinde ya ambaci alkaluman Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC), wadanda suka nuna cewa Najeriya na da jami'o'i 312 zuwa watan Yunin 2026.

Ya ce daga cikin jami'o'in akwai guda 77 na gwamnatin tarayya, guda 67 mallakar gwamnatocin jihohi da kuma guda 168 masu zaman kansu.

Dogara ya kare Shugaba Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

An kashe 'yan bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa an gano gawarwaki sama da 30 da ake zargin na ’yan bindiga ne a gonaki da ke kewaye da garin Bukuyum a Jihar Zamfara.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da hakan, ta ce an gano gawarwakin ne bayan arangama tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng