Mene Dalilin Fadan Sojoji da 'Yan Sanda da Ya Yi Ajalin Dan Sanda? Gaskiya Ta Bayyana

Mene Dalilin Fadan Sojoji da 'Yan Sanda da Ya Yi Ajalin Dan Sanda? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wani dan sanda ya rasa ransa yayin wani arangama tsakanin sojoji da 'yan sanda a jihar Adamawa
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsariniyar ta yi ajalin jami'in dan sanda mai suna Jacob Daniel
  • Wannan na zuwa ne bayan kisan wani soja mai suna Sajan Ibrahim Ali da dan sanda ya yi a 2022

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi dauki ba dadi tsakanin jami'an 'yan sanda da sojoji a jihar Adamawa.

Jami'an tsaron sun bai wa hammata iska ne a ofishin rundunar 'yan sanda da ke Yola a jihar.

Dalilin rikicin sojoji da 'yan sanda da ya yi sanadin mutuwar dan sanda
An bayyana dalilin arangama tsakanin sojoji da 'yan sanda a Adamawa. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Mene dalilin fadan sojoji da 'yan sanda?

ZagazOlaMakama ya tabbatar da cewa rikicin ya fara ne bayan dan sanda ya harbi soja a kafa a yankin Doubeli.

Kara karanta wannan

Wike zai fatattaki direbobin adaidaita a Abuja daga wata mai kamawa, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce da misalin karfe tara na dare an samu hatsaniya tsakanin sojoji daga Taraba da wasu 'yan sanda da ke binciken ababan hawa.

'Yan sandan sun bukaci sojojin su sauko kasa wanda hakan ya jawo kace-nace tsakaninsu, Tribune ta tattaro.

Daga bisani, bayan abu ya fara tsami sai dan sanda ya nuna wa sojan bindiga inda shi kuma sojan ya zaro wuka daga jikinsa.

Mutum nawa aka hallaka a fadan?

Dalilin haka dan sandan ya harbe shi a kafa yayin da aka kwashe shi zuwa asibitin kwararru don ba shi kulawa.

Daga bisani rundunar sojin ta samun labarin cewa an kama jami'inta tare da kulle shi a ofishin 'yan sanda, hakan ya saka su zuwa kwatar dan uwansu da misalin karfe 11 na dare.

Sun yi kokarin shiga hedkwatar da karfi yayin da aka fara artabu wanda ya yi sanadin mutuwar dan sanda mai suna Jacob Daniel.

Kara karanta wannan

An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da sojoji, an kashe wani sufeta a Adamawa

Kakakin rundunar 'yan sanda, Sulaiman Nguruje ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Laraba 22 ga watan Nuwamba.

Sojoji sun kai hari ofishin 'yan sanda a Adamawa

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa an samu dauki ba dadi tsakanin 'yan sanda da sojoji a jihar Adamawa.

A daren jiya Talata ce 21 ga watan Nuwamba aka samu hatsaniya tsakaninsu wanda ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel