A Kan Hanyarsu Ta Neman Mafita Bayan Shan Kaye a Zabe, 'Yan Jami'yya Su 10 Sun Mutu a Hatsarin Mota

A Kan Hanyarsu Ta Neman Mafita Bayan Shan Kaye a Zabe, 'Yan Jami'yya Su 10 Sun Mutu a Hatsarin Mota

  • Jimami yayin da wani mummunan hatsari ya rutsa da wasu magoya bayan jam'iyyar SDP a jihar Kogi
  • Matafiyan sun hadu da tsautsayin ne a yau Asabar a kan hanyarsu ta zuwa ganawar siyasa bayan faduwa zaben gwamna
  • Wannan na zuwa ne bayan jami'yyar ta sha kaye a zaben da Usman Ododo na jam'iyyar APC ya yi nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin wasu magoya bayan jam'iyyar SDP guda 10 a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a yau Asabar 18 ga watan Nuwamba a kan hanyar Anyingba zuwa Ankpa a jihar, cewar Tribune.

Magoya bayan jam'iyyar SDP sun mutu yayin wani mummunan hatsarin mota
Mutane 10 sun mutu yayin hatsarin mota a Kogi. Hoto: Yahaya Bello.
Asali: UGC

Su waye hatsarin ya rutsa da su a Kogi?

Kara karanta wannan

Da hannun Tinubu, dan takarar gwamnan Kogi ya yi amai ya lashe, ya garzaya kotu neman hakkinsa

Daga cikin wadanda su ka gamu da hatsarin mutane biyu sun samu munanan raunaka yayin da aka kwashe su zuwa asibiti mafi kusa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tattaro cewa hatsarin ya afku ne a yau da misalin karfe 10 na safe yayin da matafiyan ke kan hanyarsu ta zuwa wata ganawar siyasa.

Ganawar an shirya ta ne da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar don samo hanyar bullowa matsalar shan kaye da su ka yi a zabe.

Wane martani FRSC ta yi kan hatsarin a Kogi?

Idan ba a mantaba, a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba ce aka gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi, cewar Punch.

Dan takarar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka ya kasance na biyu a zaben yayin da Usman Ododo na APC ya lashe zaben.

Wata majiya ta ce:

"Hatsarin ya faru ne bayan motoci biyu sun ci karo da juna yayin da su ke sheka gudu."

Kara karanta wannan

INEC ta mika satifiket ga sabon gwamnan APC, ya tura muhimmin sako

Kwamitin kamfe na jam'iyyar sun jajantawa iyalan wadanda su ka mutu inda su ka yi addu'ar ubangiji ya musu rahama.

Yayin da ya ke martani, kwamandan Hukumar FRSC, Samuel Oyedeji ya ce har zuwa lokacin tattara wannan rahoto bai samu bayani kan hatsarin ba.

Ajaka ya runtuma zuwa kotu kan zaben jihar Kogi

A wani labarin, dan takarar jam'iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Kogi, Murtala Ajaka ya daukaka kara zuwa kotu.

Ajaka na kalubalantar zaben da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel