Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wasu Garuruwa a Arewa, Sun Tafka Barna da Kashe Mutum 20

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wasu Garuruwa a Arewa, Sun Tafka Barna da Kashe Mutum 20

  • Yan bindiga sun kai kazamin hari kan wasu garuruwa a yankunan Yangtu da Ussa da ke jihar Taraba
  • Harin wanda ya afku a yammacin ranar Juma'a, ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane 20
  • Rundunar yan sandan jihar Taraba ta yi martani, ta ce har yanzu lamarin na karkashin bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun kai farmaki tare da kashe mutane 20 a yankunan Yangtu da Ussa da ke jihar Taraba, a yammacin ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba.

Wasu majiyoyi daga yankunan sun tabbatarwa jaridar Punch da hakan ta wayar tarho.

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas
Yadda Rayuka 20 Suka Salwanta a Mummunan Harin da Yan Bindiga Suka Kai Wata Jihar Arewa Hoto: @GovAgbuKefa
Asali: Twitter

Wani jagoran matasa kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a Mista Ure Caleb, ya shaida wa jaridar cewa an kashe sama da mutum 20 a hare-hare mabanbanta da aka kai wasu garuruwa a kananan hukumomin Ussa da Yangtu.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun kai samame maɓoyar yan bindiga a garuruwa 6, da yawa sun sheka lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ciyaman na karamar hukumar Ussa ya tabbatar da harin

Shugaban karamar hukumar Ussa, Mista Peter Shamwun, ya bayyawa manema labarai cewa yan bindigar sun kai farmaki da kashe mutum tara a garuruwan Rubur Ribasi, Nyicwu, da Ruwah da ke Yangtu da misalin karfe 6:00 na yammacin Juma'a.

Shamwun ya ce yan bindigar sun kai hari a hanyar Takum-Ussa, inda suka kashe karin mutane, yana mai cewa maharan sun kuma farmaki garin Kpambo Yashe a karamar hukumar Ussa inda suka kashe mutum daya.

Shugaban karamar hukumar ya roki Gwamna Agbu Kefas da Shugaban kasa Bola Tinubu, da su gaggauta kawo dauki da zuba jami'an tsaro zuwa yankin don fatattakar yan bindigar.

Ya ce:

"Ban san dalilin da yasa yan bindigar suka zabi mayar da hankali a yankin ba sannan suna ta ayyukansu hankali kwance ba tare da kalubale daga jami'an tsaro ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya kaure a wata kasuwar arewa, rayuka 6 sun salwanta

"Daga wajen da aka kashe wani mutumi a yammacin jiya a Ussa zuwa sansanin soji da ke Takum, bai kai kilomita daya ba."

Ya ce yawan hare-haren da ake kai wa mutane ya kawo matsalar jin kai da rashin tsaron abinci. A cewarsa ana farmakar mutanensa a duk sanda suka je gona.

"Na yi ido hudu da mutuwa" - Wani da ya tsallake rijiya da baya a harin

Mista Yakubu Tinya wanda ya tsallake rijiya da baya yayin harin ya bayyana cewa maharan sun kuma kashe mutum daya a garin Tukwog, hanyar Takum-Manya.

Tinya ya ce

"Maharan sun zo da yawansu sannan suka farmaki garuruwa daban-daban da misalin karfe 6:00 na yamma, sannan suka kashe mutane da yawa. An farmaki wasu ne a gonakinsu, wasu a hanyarsu ta dawowa yayin da wasu a gidajensu.
"Na yi ido hudu da mutuwa amma Allah ya tsare ni. Sun farmake ni da kannena biyu. An kashe daya daga cikinmu. Maharan sun yi kama da Fulani, amma wasunsu sun yi kama da ya kasar waje."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugaban APC a jihar arewa

Rundunar yan sanda ta yi martani

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ya ce har yanzu ana kan binciken lamarin.

Rayuka sun salwanta a hatsarin kwale-kwale

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa kimanin makonni biyu baya da wani hatsarin kwale-kwale ya lakume rayuka da dama a jihar Taraba, yanzu ma mutane 8 sun mutu tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Ibi.

PREMIUM TIMES ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a kauyen Anyeshi da ke kusa da jihar Benuwe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel