Shin Ana Mutuwa a Dawo? Matashin Mawaki Ya Sake Bayyana a Faifan Bidiyo Bayan Sanar da Mutuwarshi

Shin Ana Mutuwa a Dawo? Matashin Mawaki Ya Sake Bayyana a Faifan Bidiyo Bayan Sanar da Mutuwarshi

  • Shahararren mawaki da ya rasu kwanaki 10 da su ka wuce ya sake bayyana a kafar sadarwa inda ya wallafa bidiyo
  • Mawakin wanda aka fi sani da Oladips an sanar da rasuwarshi a ranar 14 ga watan Nuwamba a shafin Instagram
  • Abin mamaki, mawakin ya wallafa sabon faifan bidiyo inda ya nuna cewa ya na raye ba kamar yadda aka yada a baya ba cewa ya mutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Matashin mawaki da ya rasu a kwanakin baya ya sake dawowa bayan bayyanarshi a kafafen sadarwa.

Marigayin mai suna Oladipopu Olabode Oladimeji da aka fi sani da 'Oladips' an sanar da rasuwarshi makwanni kadan da su ka wuce, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

Mawakin Najeriya Oladips ya sake bayyana bayan sanar da mutuwarshi
Abin mamaki bayan mawaki ya dawo bayan sanar da mutuwarshi. Hoto: @oladilpsoflife.
Asali: Instagram

Yaushe aka sanar da mutuwar matashin mawakin?

Manajan kamfaninsa ne ya sanar da mutuwarshi a shafin Instagram a ranar 14 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani kamfanin ya goge sanarwar mutuwar mawakin bayan sake bayyanar mawakin a wani sabon faifan bidiyo.

Abin mamaki mawakin ya sake bayyana bayan wallafa wani faifan bidiyo a shafin Instagram a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba.

A cikin faifan bidiyon, an gano shi da mahaifiyarsa inda ya aske kansa sabanin yadda aka sanshi a baya da gashi.

Mahaifiyar mawakin wanda a baya ta hana kai Oladips asibiti an gano ta a bidiyon ta na masa addu'a.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan mutuwar mawaki Mohbad a jihar Legas wanda ya jawo cece-kuce a Najeriya.

Daga bisani, rundunar 'yan sanda ta tono gawarsa don yin bincike kan musabbin mutuwarshi ganin yadda mutuwar ta ta da jijiyoyin wuya.

Kara karanta wannan

Wike zai fatattaki direbobin adaidaita a Abuja daga wata mai kamawa, ya fadi dalili

Matashin mawaki a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, Matashin mawaki a Najeriya, Oladipopu Olabode Oladimeji ya rasu ya na da shekaru 29 a duniya.

Marigayin wanda aka fi sani da 'Oladips' ya rasu ne a ranar 14 ga watan Nuwamba a Legas.

Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan mutuwar mawaki Mohbad wanda ya rasu shi ma a jihar Legas da aka yi ta cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel