Atiku Ya Gano Kuskuren Tinubu a Mulki, Ya Ɗauki Alƙawarin Gyara Bangaren

Atiku Ya Gano Kuskuren Tinubu a Mulki, Ya Ɗauki Alƙawarin Gyara Bangaren

  • Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Bola Tinubu da kasa cika alkawarin samar wa ’yan Najeriya wutar lantarki mai ɗorewa tun bayan hawansa mulki
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ’yan Najeriya na biyan kuɗin wutar lantarki mai tsada duk da rashin samun ingantaccen haske a gidaje da kasuwancinsu
  • Atiku ya yi alƙawarin kawo ƙarshen tsarin rukunan wutar lantarki na A zuwa E, tare da samar da tsari mai sauƙi da araha idan aka zaɓe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da Bola Tinubu.

Atiku ya zargi kwamitin da ƙoƙarin ɓoye gazawar Shugaba Bola Tinubu wajen cika alkawarin samar da wutar lantarki mai ɗorewa, ta hanyar jerin dokoki da ayyuka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Atiku ya dura kan Tinubu
Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Atiku Abubakar, Dada Olusegun.
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, ya fitar, Atiku ya ce bai kamata APC ta riƙa bikin takardu ba yayin da gidaje da kasuwanci ke cikin duhu.

Ya ce bayan shekaru uku da rabi, iyalai na fama da matsalar samun hasken lantarki a gidajensu, yayin da ’yan kasuwa ke kashe kuɗaɗe wajen samar da wutar lantarki.

Atiku ya ce ƙananan ’yan kasuwa na amfani da kuɗaɗen da ba su da yawa wajen sayen madadin wutar lantarki, amma har yanzu suna fuskantar barazanar durƙushewar kasuwancinsu.

Ya ƙara da cewa ana cajin ’yan Najeriya kuɗin wutar lantarki duk da cewa ba za su iya dogaro da samun hasken ba. Ya ce Tinubu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki mai ɗorewa da kuma kawo ƙarshen tsarin ƙiyasta kuɗin wuta, amma bai cika ba.

A faɗin Najeriya, ana sanya masu amfani da wutar lantarki cikin rukunan A, B, C, D da E, inda ake cajin su kuɗaɗe daban-daban.

Kara karanta wannan

Atiku ya zargi Tinubu da shirin tafiya Faransa amma ya fake da zuwa Saudi

A wasu yankuna, masu amfani da Band A na biyan kusan Naira 209.50 kan kowace unit kafin harajin VAT. Kuɗin sauran rukunan kuma ya bambanta bisa jiha da kamfanin rarraba wutar lantarki.

Sai dai ya ce duk da bambancin farashin, matsalar iri ɗaya ce a dukkan rukunan: wutar lantarki na yankewa, amma takardar kuɗin biya tana zuwa.

Atiku ya ce bai kamata iyali su riƙa zaɓar tsakanin kuɗin wutar lantarki da kuɗin sayen abinci ba. Haka kuma, bai kamata kasuwanci ya riƙa biyan kuɗi mai yawa yana samun ƙarancin wuta ba.

Ya ce gwamnatin Tinubu yanzu ta bayyana shirin kawo ƙarshen tallafin wutar lantarki daga shekarar 2027, duk da cewa tana cewa ba za a ƙara kuɗin wuta nan take ba.

Atiku ya ce ’yan Najeriya na da haƙƙin samun cikakken bayani kan abin da zai faru da kuɗin wutar lantarkinsu bayan cire tallafin.

Ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi, zai yi aiki da gwamnatocin jihohi da hukumomin da ke kula da wutar lantarki, bisa doka, domin soke tsarin rukunan wutar lantarki na yanzu.

Ya ce zai maye gurbinsa da tsari mai adalci, bayyananne kuma mai sauƙin biya, wanda zai kare iyalai tare da tilasta wa kamfanonin wutar lantarki ɗaukar alhakin hasken da suke samarwa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Atiku ya jaddada cewa samar da wutar lantarki mai ɗorewa da ’yan Najeriya za su iya biya zai kasance cikin manyan abubuwan da zai ba fifiko a ƙasa.

Ya tunatar da cewa lokacin yaƙin neman zaɓen 2022, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki a kowane lokaci cikin shekaru huɗu.

Tinubu ya ce:

“Idan na kasa samar muku da wutar lantarki a kowane lokaci cikin shekaru huɗu, idan na dawo neman wa’adi na biyu, kada ku zaɓe ni.”

Atiku ya ce ’yan Najeriya sun shafe waɗannan shekaru huɗu, don haka ba sa buƙatar kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya fassara musu kalaman Tinubu. Abin da suke buƙata shi ne ya amsa musu.

Ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu ba ta gina ko da wata sabuwar cibiyar samar da wutar lantarki da kanta ba domin ƙara ƙarfin wutar lantarkin Najeriya.

Sai dai ya ce gwamnatin ta ƙaddamar da shirin sayar da takardun lamuni na tiriliyoyin Naira domin biyan tsoffin basussukan da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki.

Atiku ya ce har yanzu ba a bayyana wa ’yan Najeriya yadda wannan matakin kuɗi ya taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ɗorewa da aka yi musu alkawari ba.

Kara karanta wannan

Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki

Ya jaddada cewa biyan tsoffin basussuka ba ɗaya yake da gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ba. Ya ce bai kamata a maye gurbin wutar lantarki da takardun lamuni ba.

A halin da ake ciki, Atiku ya ce ’yan Najeriya na fuskantar harajin VAT kan wutar lantarki, yayin da dokar harajin Najeriya ta tanadi ƙarin harajin kashi biyar cikin ɗari kan wasu makamashin da ake samu daga burbushin halittu, ciki har da fetur da dizal.

Atiku ya tura bukata ga INEC

An ji cewa Atiku Abubakar ya soki INEC bayan amincewa da cewa jami'anta sun shigar da hotunan da AI ta samar da bayanan bogi cikin rajistar masu kada kuri'a.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci INEC ta bayyana sunayen jami'an da ake zargi, ta fitar da hujjoji tare da mika wadanda abin ya shafa ga hukumomin tsaro.

Atiku ya ce zargin cewa hotunan AI sama da miliyan 20 na iya kasancewa cikin rajistar ya sa ya zama wajibi a gudanar da binciken fasaha mai zaman kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.