Sarkin Musulmi Ya Naɗa Ɗansa, Babban Malamin Musulunci Sarauta a Sokoto

Sarkin Musulmi Ya Naɗa Ɗansa, Babban Malamin Musulunci Sarauta a Sokoto

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya naɗa ’ya’yansa biyu da wasu fitattun mutane sarautun gargajiya a jihar Sokoto
  • Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai fitaccen attajiri kuma malamin addinin Musulunci, Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya, da Farfesa Mansur Ibrahim
  • Sarkin Musulmi ya ce ya ba su sarautun ne bisa cancanta, gudunmawarsu ga al’umma, tare da bukatar amfani da matsayinsu wajen inganta zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya naɗa ’ya’yansa biyu, wani fitaccen mai taimakon jama’a, malamin addinin Musulunci da sauran manyan mutane sarautun gargajiya.

An naɗa ’ya’yansa biyu, Abubakar Sadiq Abubakar da Shehu Usman Abubakar, sarautun Sarkin Dawaki Tsakar Gida da Fagachin Sokoto, a wani bikin musamman ranar Lahadi.

Sarkin Musulmi ya yi nadin sarauta
Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Twitter

Sheikh Mansur ya samu sarauta a Sokoto

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya mika sandar mulki ga sabon Sarkin Gusau da wasu sarakuna 18

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da fitaccen mai taimakon jama’a kuma malamin addinin Musulunci, Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya, a matsayin Dallatun Sokoto, da Farfesa Mansur Ibrahim a matsayin Danmasanin Sokoto, cewar Daily Trust.

An kuma naɗa Alhaji Abubakar Hussain a matsayin Sarkin Bai, Alhaji Aminu Isa-Buhari a matsayin Danmalikin Sokoto, sannan Farfesa Ishaq Oloyede a matsayin Kuliyan Sokoto.

Haka kuma, an naɗa Dakta Peter Igoh a matsayin Kakakin Daular Usmaniyya, yayin da Hon. Almustapha Rabah ya samu sarautar Bauran Sokoto.

Sauran waɗanda suka samu sarautun sun haɗa da Dakta Balarabe Kakale a matsayin Wakilin Makarantar Daular Usmaniyya da Alhaji Bello Abbas.

An kuma naɗa Alhaji Gandi Umar a matsayin Sarkin Galmar Sarkin Musulmi, yayin da Alhaji Abdulqadir Bello-Jeli ya zama Sarkin Fulotin Sokoto.

Da yake jawabi a wajen bikin, Sarkin Musulmi ya ce ya naɗa waɗanda suka samu sarautun ne bisa cancanta da gudunmawarsu ga al'umma, tare da la'akari da nasarorin da suka samu.

Mai martaban ya buƙaci waɗanda aka naɗa da su ɗauki sarautun a matsayin ƙarin nauyin hidimtawa al'umma, jajircewa da ɗaukar nauyi, ba kawai wata alamar girmamawa ba.

Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa wajen amfani da matsayinsu domin inganta zaman lafiya, haɗin kai, fahimtar juna tsakanin addinai da ci gaban Daular Usmaniyya da ƙasar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da rasuwar babban dan kasuwa a Kano

Da yake magana da manema labarai bayan naɗinsa, Dan’iya ya nuna godiyarsa ga Sarkin Musulmi bisa ganin cancantarsa da ba shi sarautar Dallatun Sokoto.

Ya bayyana sarautar a matsayin wata babbar dama da karramawa, inda ya yi alƙawarin ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban al'umma, musamman taimakon jama'a.

Ya ce zai mayar da hankali kan ayyukan agaji, harkokin addini da tallafa wa marasa galihu domin inganta rayuwarsu.

Bikin ya samu halartar manyan mutane daga cikin Najeriya da wajen ƙasar, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas da sauran manyan baƙi.

Sarkin Musulmi ya ba Igho sarauta

An ji cewa Sarkin Musulmi zai nada Chief Peter Igho a matsayin Kakakin Daular Usmaniyya a wani bikin da za a gudanar a fadarsa da ke Sokoto.

An ba Igho sarautar ne tun ranar 10 ga Satumba, 2025, saboda gudummawar da ya bayar ga majalisar masarautar, Jihar Sokoto da Najeriya.

Igho ya shahara wajen shirya shirin talabijin, tare da horar da tsararrun kwararru a fannin yada labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.