Allah Ya Karbi Rayuwar Shahararren Malamin Addinin Musulunci a Gombe

Allah Ya Karbi Rayuwar Shahararren Malamin Addinin Musulunci a Gombe

  • Jimami yayin da aka yi babban rashi na shahararren malamin addinin Musulunci a jihar Gombe
  • Marigayin Imam Saidu Abubakar ya rasu da safiyar yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba a birnin Gombe
  • Kafin rasuwar marigayin shi ne babban limamin masallacin Izala na biyu da ke Abuja Low Cost a cikin Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - An tafka babban rashi bayan rasuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Gombe.

Marigayin mai suna Imam Sa'id Abubakar ya rasu a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba a birnin Gombe.

Shahararren malamin addinin Musulunci, Imam Sa'idu ya riga mu gidan gaskiya
Allah Ya Karbi Rayuwar Malamin Addinin Musulunci a Gombe. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rasu a jihar Gombe?

Kafin rasuwarshi, marigayin shi ne babban limamin masallacin Izala na biyu da ke Abuja Low Cost a Gombe, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, Sifeta ya kadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu na kusa da marigayin sun bayyana shi a matsayin mutum wanda ya ta'allaka rayuwarsa ga hidimar addinin Musulunci.

Marigayin ya rasu da safiyar yau Juma'a ya na da sheakru 71 a duniya bayan gwagwarmaya wa addini.

Wane martani Gwamna Inuwa kan rasuwar marigayin?

Yayin mika jaje ga iyalan marigayin, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya nuna kaduwarshi da wannan rashi na babban malami.

Inuwa ya bayyana mutuwar malamin a matsayin babban rashi da ya janyo gibi wanda zai yi wahalar cike wa, Arewa Reporters ta tattaro.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Isma'ila Uba Misillli ya fitar ya bayyana irin tarun ilimi da gudunmawar malamin da cewa ba za mance da su ba.

A karshe ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin ya kuma saka masa da gidan aljanna saboda irin aikin alkairi da ya yi wa addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan 'Boko Haram' sun budewa ayarin motoccin Gwamna Buni wuta, rayuka sun salwanta

Samanja mazan fama ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, Shahararren dan wasan kwaikwayo, Alhaji Usman Baba Pategi ya riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar da ta gabata.

Marigayin wanda aka fi sani da Samanja mazan fama ya rasu bayan fama da doguwar jinya a Kaduna.

Samanja wanda kuma tsohon soja ne ya shafe shekaru da dama ya na wasan kwaikwayo a gidan rediyon Najeriya ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel