Abun Al Ajabi
Wani yaro da ke rabe-rabe a titin Lagas tsawon shekaru shida tare da samawa kansa abun da zai ci ya samu tagomashin alkhairi daga mutanen da suka ji labarinsa.
Wani mutum ya dauki hankalin jama’a bayan ya kama wani katon kifi. Ya kinkimo kifin a kan kafadunsa. Mutane da ke wajen sun zura mai ido yayin da yake wucewa.
Wasu ma’aurata da suka shafe shekaru 17 tare sun gano cewa su din yan uwa ne kuma mutane sun shawarce su da su rabu bayan sun haifi yara uku a tare. Sun ce sam.
Dan Chinan da ake zargi da kashe budurwarsa a jihar Kano ya amsa laifinsa, inda yace da kansa ya kashe Ummita yayin da ya farde ta da wuka ta mutu har lahira.
Wata budurwa ta girgiza jama'a yayin da ta dauki ruwa a lokacin da aka bata damar daukar komai take so a kantin siyayya da ke wata jiha a Najeriya, ta kwafsa.
Wata dattijuwar mata ta haifi yan uku tana da shekaru 54 a duniya kuma ta wallafa bidiyo domin murnar haihuwar yaran, tuni bidiyon ya yadu a soshiyal midiya.
Wani uba ya kirkiri sabuwar hanyar shayar da karamin dansa a bayan idon mahaifiyarsa, ya yi amfani da wani dabara da ya burge mutane da dama da basu dariya.
Wata budurwa yar Najeriya ta roki saurayinta a kan kada ya rabu da ita bayan ta kama shi yana cin amanarta. Ta saki hirarsu ta WhatsApp dake nuna tana rokonsa.
Wani matashi dan Najeriya ya wallafa bidiyon kerarren gidan da ya ginawa mahaifiyarsa. Ya ce yana dauke da dakunan bacci guda biyar. Mutane sun taya shi murna.
Abun Al Ajabi
Samu kari