Ribadu Ya Fadi Yadda 'Yan Ta'adda ke Aiki da AI da Kirifto Su Tara Kudi da kai Hari

Ribadu Ya Fadi Yadda 'Yan Ta'adda ke Aiki da AI da Kirifto Su Tara Kudi da kai Hari

  • Mai Bada Shawara kan Tsaron Ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, da AU sun yi gargaɗi cewa 'yan ta'adda suna amfani da hanyoyin sadarwa da fasahohin zamani
  • Ribadu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron horaswa na yankin Yammacin Africa da Sahel kan hanyoyin ganowa tare da murƙushe 'yan ta'adda
  • AU ta buƙaci a haɗa kai da kamfanonin sadarwa da na kafen sada zumunta domin gano hanyoyin da 'yan ta'addar ke amfani da su wajen sayen makamai a ɓoye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai bada shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙungiyoyin 'yan ta'adda ke ƙara dogaro da fasahohin zamani irin su AI, Kirifto, da jirage marasa matuka wajen gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

NCC ta ɓullo da wani tsari, mutane na iya asarar wayoyin da suka Ssaya da kuɗinsu a Najeriya

Ribadu, wanda Babban Jami'in Gudanarwa na Cibiyar Ƙasa ta Ƙalubalantar Ta'addanci (NCTC), Maj Gen Adamu Laka ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe taron horaswa na kwana uku a Abuja.

Malam Nuhu Ribadu
NSA na Najeriya, Malam Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

'Yan ta'adda na aiki da fasaha

Punch ta rahoto cewa Nuhu Ribadu ya jaddada cewa amfani da fasahohi irin su AI wajen ƙirƙirar saƙonnin yaudara da kuma amfani da Kirifto wajen gudanar da mu'amalar kuɗi ya ƙara sarƙaƙiya ga kalubalen tsaron a Najeriya.

Gudanar da bincike da gano waɗannan barazana yana buƙatar haɓaka ƙwarewar jami'an tsaro da ma'aikatu maimakon kawai sayen kayan aiki na zamani.

Ribadu ya ƙara da cewa Najeriya tana aiki kafada da kafada da ƙungiyar AU domin mayar da cibiyar NCTC ta zama zakara a fannin yaƙi da ta'addanci a yankin Yammacin Africa da Sahel.

Bayanin jami'in kungiyar AU

A gefe guda, Muƙaddashin Darakta na Cibiyar Yaƙi da Ta'addanci ta AU, Idriss Lalalli, ya ce ƙungiyoyi irin su ISWAP, Boko Haram da JNIM suna yaɗa aikace-aikacensu ta kafafen sada zumunta da kasuwannin ɓoye a intanet don sayen makamai.

Lalalli ya nuna cewa saurin da waɗannan 'yan ta'adda ke bi da kuma ƙarancin kuɗin da suke kashewa wajen yin hakan yana ba su damar tsallake matakan tsaro cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Babban dalilin da ya sa Atiku ya kayar da Tinubu a zaɓen 2023 a Kaduna'

A bayanin da ya yi, ya nemi a gaggauta horar da jami'ai kan gano barazanar yanar gizo da nazarin sauran abubuwan da ke da alaka da fasaha.

Nuhu Ribadu a Amurka
Lokacin da Nuhu Ribadu ya ziyarci Amurka kan tsaron Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ina aka kai kudin makamai?

A wani labarin, mun ruwaito cewa Tukur Buratai ya bayyana cewa dalar Amurka biliyan 1 da gwamnatin tarayya ta amince da ita don siyan kayan tsaro a zamaninsa ba ta ratsa ta hannun rundunonin soji ba.

Buratai ya tabbatar da cewa kuɗin da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) ta amince da su an mika su ne kai tsaye ga Ma'aikatar Tsaro ta Ƙasa.

Ya ƙara da cewa zargin da aka yi ta yaɗawa na cewa an karkatar da kuɗin don harkar zaɓe ya kasance ne sakamakon siyasa da ƙirƙirar jita-jita lokacin zaɓen shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng