Maganar INEC kan Fasahar AI a Zabe Ya Jawo Magana, NDC Ta Gano Shirin Hukumar
- Jam’iyyar NDC ta zargi INEC da shirin amfani da fasahar AI wajen maguɗin zaɓen 2027 domin fifita jam’iyyar APC mai mulki
- Mai magana da yawun NDC, Osa Director, ya tambayi dalilin da INEC ke son amfani da AI ba tare da gwada ingancinta ba
- NDC ta nuna damuwa kan gaggawar shigar da AI cikin zaɓe, tana tambayar dalilin da INEC ba ta gwada fasahar a zaɓen Osun ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) game da zaben 2027.
Jam'iyyar NDC na zargin INEC da shirin amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) wajen yin maguɗi a babban zaɓen Najeriya na 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da wakilin Legit Hausa ya gano wanada jam'iyyar ta wallafa a shafin X a yau Alhamis 15 ga watan Oktobar 2026.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Osa Director, ya ce INEC na shirin yin maguɗin zaɓen domin fifita jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Maganar INEC kan fasahar AI
A baya, shugaban INEC, Joash Amupitan, ya bayyana a wani taron manema labarai na duniya cewa hukumar na shirin amfani da fasahar AI a babban zaɓen 2027.
Sai dai Director ya nuna shakku kan yadda INEC za ta iya amfani da AI wajen magance matsalolin zaɓe yadda ya kamata, alhali gwamnati ta kasa amfani da irin wannan fasaha wajen shawo kan matsalar rashin tsaro.
Director ya bayyana cewa INEC ba ta yi abin da ya kamata ba wajen tabbatar da cewa fasahar a shirye take don amfani da ita a babban zaɓe.

Source: Facebook
Shakkun da NDC ta nuna kan INEC
Ya nuna cewa hukumar ba ta gwada kayan aikin AI ba a duk wani zaɓen gwamna da aka gudanar ba a lokacin babban zaɓe.
Ya bayyana zaɓen gwamnan jihar Osun a matsayin damar da hukumar ta rasa wajen gwada irin wannan fasaha kafin zaɓen 2027.
Ya ce:
“Ga ƙasar da har yanzu ba ta iya amfani da AI wajen magance matsalolin tsaro masu sarkakiya da take fama da su ba, shin batun zaɓen shugabannin gwamnati ne kawai za ta iya warwarewa ta amfani da AI?”
Haka kuma, ya soki abin da ya kira gaggawar shirin fara amfani da fasahar, yana mai cewa hukumar ba ta ware isasshen lokaci don tabbatar da inganci da sahihancin fasahar kafin zaɓen ba.
A cikin sanarwa da aka wallafa a shafin X, kakakin NDC ya ce:
“INEC na shirin yin maguɗi a babban zaɓen 2027 domin fifita APC mai lalata ƙasa, ta hanyar amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI), kwatsam, AI ta zama wata fasaha da hukumar gudanar da zaɓe ke sha’awar amfani da ita.
“Me ya sa ake gaggawar amfani da AI a babban zaɓen da ke tafe, alhali saura ƙasa da kwanaki 100? Akwai abin da ba daidai ba."
Kaduna: NDC ba ta da dan takarar gwamna
A baya, an ji cewa jam’iyyar NDC ba ta da wanda zai yi mata takarar gwamnan jiha a Kaduna a zaben da za a yi a badi.
Bayan fitar da sunayen, ba a ga sunan Danjuma Laah ba da hukumar INEC ta saki jerin karshe na masu neman takara.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Kudu, Laah aka yi tunanin zai kalubalanci APC da ADC a zaben Kaduna mai zuwa a 2027.
Asali: Legit.ng


