“Aiki Ya Yi Kyau”: Uba Ya Samo Dabarar Shayar Da Dansa a Bayan Idon Mahaifiyarsa

“Aiki Ya Yi Kyau”: Uba Ya Samo Dabarar Shayar Da Dansa a Bayan Idon Mahaifiyarsa

  • Wani bidiyon TikTok da ke nuna wani uba yana shayar da dansa cikin dabara ya tsuma zukata da dama
  • A bidiyon, uban ya sanya hoto da ke dauke da fuskar mahaifiyar yaron a nashi fuskan sannan ya makala fida a kirjinsa
  • Karamin yaron da ya fada tarkon mahaifin nasa ya sha madarar nasa hankali kwance yana mai tunanin da gaske mahaifiyarsa ce ke shayar da shi

Wani uba ya shirya wata dabara don tabbatar da ganin cewa karamin dansa ya karbi abincinsa a bayan idon mahaifiyarsa kuma hakan ya haifar da martani masu yawan gaske.

A bidiyon da ya yadu, mahaifin yaron ya dauki babban hoton fuskar matarsa sannan ya makala a nasa fuskan inda ya kuma dauki fidan yaron ya sakala a kirjinsa don nuna cewa ruwan nono ne ke fita daga jikinsa.

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Samu Cikin Fari Tana Da Shekaru 54, Allah Ya Azurta Ta Da Yan Uku a Bidiyo

Uba yana shayar da dansa cikin dabara
“Aiki Ya Yi Kyau”: Uba Ya Samo Dabarar Shayar Da Dansa a Bayan Idon Mahaifiyarsa Hoto: @lovelybabydaily
Asali: UGC

Alamu sun nuna yaron bai fahimci wayon da aka yi masa ba domin dai ya mayar da hankali wajen tsotson fidansa.

Karamin yaro ya fada tarkon mahaifinsa

Ga dukkan alamu, ta wannan hanyar ne kadai yaron zai karbi madararsa a bayan idon mahaifiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu amfani da TikTok da dama da suka kalli bidiyon sun yaba ma kokarin uban kuma sun ce za su yi amfani da irin haka.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tattara 'likes' fiye da 100,000 da martani fiye da 1000 a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@user5262 ya yi martani:

"Ka ci jarrabawar dadi."

@giltiusexclusive ta ce:

"Uban shekara."

@jane3637 ya rubuta:

"Wannan irin tunani mai cike da hikima, na so shi."

@jhanteeputanya ta yi martani:

"Aiki ya yi kyau."

@christek ta yi martani:

"Uwar da ta fi kowa."

Kara karanta wannan

“Duk Naki Ne Uwata”: Matashi Ya Kerawa Mahaifiyarsa Hadadden Gida, Bidiyon Ya Dauki Hankali

Magidanci ya gudu ya bar matarsa saboda gemu ya tsiro mata a fuska

A wani labari na daban, wata mutuniyar kasar Indiya mai suna Mandeep Kaur ta bayyana yadda mai gidanta ya gudu ya barta saboda gemu ya tsiro mata a fuska inda ta koma tamkar namiji.

Kaur ta ce da farko ta shiga mawuyacin hali tare da tsananin kunyar kanta domin dai bata da wani banbanci da 'da namiji amma zuwa wani lokaci sai ta karbi kanta a yadda take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel