“Haihuwana Na Farko Kenan”: Dattijuwa Yar Shekaru 54 Ta Haifi Yan Uku a Bidiyo

“Haihuwana Na Farko Kenan”: Dattijuwa Yar Shekaru 54 Ta Haifi Yan Uku a Bidiyo

  • Allah ya albarkaci wata yar Najeriya da bata taba haihuwa ba da kyawawan yara har guda uku a lokaci daya
  • Dattijuwar mai shekaru 54 ta wallafa wani bidiyo a TikTok don nuna yadda ta yi goyon ciki da kuma haihuwar yaran
  • Tuni labarin haihuwarta a wannan shekaru ya yadu kuma ya ba mutane da dama a soshiyal midiya mamaki

Wata dattijuwa yar Najeriya na cikin yanayi na farin ciki yayin da Allah ya albarkaceta da samun haihuwar yan uku.

Bayan isowar kyawawan yaran duniya, matar mai suna @funmiedeni ta garzaya dandalin TikTok don nuna yadda ta yi goyon cikinta a bidiyo.

Uwa da yaranta yan uku
“Haihuwana Na Farko Kenan”: Dattijuwa Yar Shekaru 54 Ta Haifi Yan Uku a Bidiyo Hoto: TikTok/@funmiedeni.
Asali: TikTok

A bidiyon mai tsawon minti 1 da sakan 20, matar ta taka rawar farin ciki yayin da take baje kolin tulun cikinta a kaya daban-daban.

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Jama'a sun kadu bayan ganin mutumin da ya reni zakanya tsawon shekaru 11

Yar Najeriya ta haihu tana da shekaru 54

Baya ga hoton tulun cikinta, matar ta kuma nuna hotunan kyawawan yaranta yan uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar matan, wannan shine haihuwanta na fari tana da shekaru 54. Hakan ya bai wa mutane da dama mamaki cewa ta dauki ciki a irin wannan shekarun.

Wadanda suka kalli bidiyon sun bayyana haihuwar yaran a matsayin mu'ujizar Ubangiji kuma sun yi addu'an samun irin haka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Princess_tabith ta ce:

"Ina rokawa abokiyar aikina irin wannan. Shekarunta 50 yanzu amma bata da haihuwa. Tana kula da yan biyu na kamar nata. Allah ya duba ki uwata."

@queensofia ta ce:

"Ina taya ki murna. Nice ta gaba a kan layi."

@kelechukwu ta ce:

"Abu ya yi kyau! Yesu baya taba gajiyawa da nuna mu'ujiza."

Kara karanta wannan

Toh fa: Mutumin da ya ba da maniyyinsa aka haifi yara sama da 500 zai fuskanci tuhumar kotu

@solabo ta ce:

"Ina tayaki murna. Babu abun da ya fi karfin Allah."

user6978269496062 ya yi martani:

"Godiya ga Allah. Allah ya sa ki ci ribar haihuwarki da sunan Yesu. Amin!"

Uba ya yi amfani da dabara wajen shayar da dansa a bayan idon matarsa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani uba ya kirkiri sabuwar hanyar shayar da dansa a bayan idon matarsa inda ya yi amfani da hoton fuskarta.

Mutumin dai ya nada hoton fuskar mahaifiyar dan jikin nasa sannan ya makala fidan a kirjinsa tamkar dai mai shayar da nono, kuma dabarar ta ki aiki sosai a kan yaron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel