“Duk Naki Ne Uwata”: Matashin Miloniya Ya Dankara Gida Mai Dakuna 5

“Duk Naki Ne Uwata”: Matashin Miloniya Ya Dankara Gida Mai Dakuna 5

  • Wani dan Najeriya ya wallafa bidiyon gidan da ya kerawa mahaifiyarsa, kuma mutane na ta taya shi murna
  • Matashin ya ce mahaifiyarsa kadai ce ta cancanci irin wannan tagomashin yayin da ya hasko ginin da aka yi wa fenti
  • Daga cikin masu amfani da TikTok da suka taya shi murna harda wani mutum da ya yaba ma yadda aka yi rufin gidan

Wani matashi dan Najeriya, @dozzy039, ya sha ruwan yabo daga wajen mutane bayan ya wallafa bidiyon sabon gidan da ya kera.

Ya yi wa bidiyon lakabi da "Duk naki ne mama babu wanda ya cancance shi" don nuna cewa mahaifiyarsa ya kerawa gidan. Bidiyon ya nuna cewa an rigada an kammala ginin kuma har an yi fentin ko'ina.

Matashi, mahaifiyarsa da hadadden gidan da ya kera mata
“Duk Naki Ne Uwata”: Matashin Miloniya Ya Dankara Gida Mai Dakuna 5 Hoto: @dozzy039
Asali: TikTok

Matashi ya yi wa mahaifiyarsa kyautar dankareren gida

Kara karanta wannan

Matashin Miloniya Ya Kera Hadadden Gida Mai Kama Da Aljannar Duniya, Bidiyon Ya Dauka Hankali

Abun da ya rage kawai ba a yi wa katafaren ginin ba shine katange shi da kuma simintin harabar gidan. Ya bayyana cewa gida ne mai dauke da dakunan bacci guda biyar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan Najeriya da dama sun garzaya sashinsa na sharhi domin taya matashin murna. Wasu sun yi addu'an Allah ya yi masu irin wannan ni'imar nan ba da dadewa ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@omodano ya ce:

"Ina tayaka da mama murna. Dan Allah tsawon wani lokaci ya dauki masu aikin kammala rufin gidan?"

@mbaemmanuel987 ya ce:

"Baaba mutumin da ya yi rufin ginin nan ya cancanci a bashi lambar yabo na rantse ina taya ka murna nima ina rokon samun irin na'imar da Allah ya yi maka."

@Oficial_p4 ya ce:

"Dan uwa na so wannan tsarin ginin ya za a yi na samu irinsa ga mahaifiyata."

Kara karanta wannan

Dan Amana: Yadda Kare Ya Taya Uwar Dakinsa Diban Ruwa Tare Da Tafasa Mata Shi, Bidiyon Ya Yadu

@thankgodwisdom3 ya ce:

"Ina tayaka murna dan uwa, nima Allah ya yi mun irin wannan ni'imar."

@horlar connect247 ya ce:

"Ina tayaka murna mai gida,, dan Allah dakuna nawa ne a ciki yallabai shakka babu na so gidan nan."

Ya amsa da:

"Manyan dakunan bacci 5."

@tlightmoney777 ya ce:

"Kai namijin duniya ne dan uwa ina tayaka murna dan uwa karin gida na nan zuwa."

Matashin miloniya ya gwangwaje kansa da katafaren gida, ya kira fasto ya sa tabarraki

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa jama'a a soshiyal midiya sun taya wani matashin dan Najeriya murna bayan ya kerawa kansa wani katafaren gida mai kama da aljannar duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel