Kwana 1 bayan Kaddamar da Kamfe, Tsohon Shugaban NPA Ta Kasa Ya Fice daga APC a Kano
- Tsohon shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Aminu Dabo, ya yi murabus daga jam'iyyar APC nan take
- Dabo, wanda ya taɓa jagorantar APC a ƙaramar hukumar Dambatta ta Jihar Kano, ya bayyana matakin a cikin wasiƙar da ya rubuta
- Tsohon kwamishinan filaye na Kano ya ce ya yanke shawarar ne bisa wasu dalilai na kansa da kuma shirye-shiryensa na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Arc. Aminu Dabo, ya yi fice daga jam'iyyar APC nan take.
Dabo, wanda ya taɓa zama shugaban kwamitin APC a ƙaramar hukumar Dambatta ta Jihar Kano, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar a cikin wata wasiƙa da ya mika wa shugabanni.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wasikar, mai dauke da kwanan watan 7 ga Oktoba, 2026, ya aika ta ga shugaban jam'iyyar APC na mazabar Dambatta Gabas.
Aminu Dabo ya fice daga APC
A cikin wasiƙar wacce ta bayyana yau Alhamis, Dabo ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan yin nazari sosai kan wasu dalilai na kansa da kuma abubuwan da yake shirin cimmawa a nan gaba.
Ya tabbatar da cewa ya miƙa wasiƙar murabus ɗinsa ga jami'an jam'iyyar APC da suka dace a Dambatta domin ɗaukar matakan da suka dace.
Tsohon shugaban na NPA ya nuna godiyarsa ga shugabannin APC bisa damar da suka ba shi ta yi wa jam'iyyar hidima, da kuma goyon baya da amincewar da suka nuna masa.
Aminu Dabo ya ce:
“Ina ci gaba da mika godiya saboda kyakkyawar alaƙar da na more, da kuma ƙwarewar da na samu a lokacin da nake yi wa jam'iyyar APC hidima.”
Ya kuma gode wa shugabannin jam'iyyar APC bisa ba shi damar bayar da gudummawa wajen ci gabanta da bunƙasarta.

Source: Twitter
Takaitaccen Tarihin Aminu Dabo
Aminu Dabo ya taɓa neman takarar gwamnan Jihar Kano, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan filaye na jihar a baya.
Haka kuma, shi ne mamallaki kuma shugaban kwalejojim lafiya guda biyu da suka hada da, Aminu Dabo College of Health Sciences and Technology da Aminu Dabo College of Nursing Sciences, waɗanda dukansu ke Kano.
Ana ganin tafiyar wannan babban jigo na iya zama koma baya ga jam'iyyar APC a jihar Kano da ma Najeriya baki daya yayin da ake shirye-shiryen babban zaben 2027.
APC ta nada kwamaitin kamfe a Kano
Kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta fitar da kwamitin da zai yi mata aikin yakin neman zaben shugaban kasa da gwamna a jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ya fitar da sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben 2027, sanda ya kunshd mutane 155.
Jerin yana kunshe da tsofaffin gwamnonin Kano, sanatoci masu-ci da wadanda aka yi a baya da suke ckin jam’iyyar APC mai mulki.
Asali: Legit.ng

