'Babban dalilin da Ya Sa Atiku Ya Kayar da Tinubu a Zaɓen 2023 a Kaduna'

'Babban dalilin da Ya Sa Atiku Ya Kayar da Tinubu a Zaɓen 2023 a Kaduna'

  • Mai magana da yawun APC a Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya yi magana kan rashin nasara da Bola Tinubu ya yi a zaben 2023 a jihar
  • Haruna ya ce salon mulkin Gwamna Uba Sani ya sauya siyasar Kaduna, inda ya haɗa mutane daga addinai, ƙabilu da jam'iyyun siyasa daban-daban
  • APC ta ce tana fatan samun ƙuri'u miliyan biyu a Kaduna domin sake zaɓen Tinubu a 2027, tare da shirya babban gangamin kamfen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sakatare mai yaɗa labarai na jam'iyyar APC a Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya yi magana kan rashin nasarar Bola Tinubu a Kaduna a 2023.

Haruna ya danganta nasarar 'yan adawa a zaɓen 2023 da rashin gamsuwar jama'a da gwamnatin tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Wai Trump ya nemi afuwar Tinubu kan wasu zarge zarge? Ga abin da aka binciko

An fadi dalilin faduwar Tinubu a zaben 2023 na Kaduna
Shugaba Bola Tinubu da dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Mai magana da yawun APC ya bayyana hakan ne yayin ganawa da 'yan jarida kan shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kaduna, cewar Vanguard.

2023: Abin da jawo faduwar Tinubu a Kaduna

Za a tarbe shi ne domin ƙaddamar da kamfen ɗin jam'iyyar na zaɓen shugaban ƙasa na 2027, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 24 ga Oktoba, 2026.

Haruna ya ce sakamakon zaɓen ya nuna rashin jin daɗin masu zaɓe da salon mulkin tsohon gwamnan, wanda ya zarga da rushe gidaje da kasuwanni, korar dubban ma'aikata da kuma amfani da bambance-bambancen addini da ƙabila.

Ya ce yanayin siyasar ya sauya a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani, wanda gwamnatinsa ta rungumi salon mulki mai haɗa kowa, tare da jawo mutane daga addinai, ƙabilu da jam'iyyun siyasa daban-daban zuwa APC.

Haruna ya ce:

"Yawancin zaɓe yakan zama tamkar ƙuri'ar amincewa ko rashin amincewa da shugabanci a wani lokaci na tarihi. Saboda haka, zaɓen Kaduna na 2023 ya kasance ƙuri'ar auna salon mulkin tsohon gwamnan jihar.”

Kara karanta wannan

Pantami ya tara manyan lauyoyi sun tunkari INEC kan cire sunan shi

Ya ƙara da cewa manufofin gwamnatin da ta gabata sun sa wasu sassan jihar suka juya mata baya, musamman Kudancin Kaduna, inda masu zaɓe suka daɗe suna goyon bayan jam'iyyun adawa.

Ya ce:

“Mutanen jihar ba su ji daɗin salon mulkin wannan gwamna ba a wancan lokacin.”
An yaba wa salon mulkin Uba Sani a Kaduna
Gwamna Uba Sani yayin ziyara ga Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Sauyin da mulkin Uba Sani ya kawo

Haruna ya yi ikirarin cewa salon mulkin Gwamna Uba Sani ya sauya yanayin siyasar jihar, inda ya ce yanzu APC ce ke riƙe da dukkan muƙaman zaɓe a Kaduna.

Ya ce gwamnan ya nuna girmamawa ga mutane ba tare da la'akari da addininsu, ƙabilarsu, matsayinsu na tattalin arziki ko al'adunsu ba.

Ya ƙara da cewa hakan ya ƙarfafa mutane da dama su rungumi jam'iyyar mai mulki, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A cewarsa, matsayin APC a siyasar Kaduna a yanzu ya bambanta da yadda yake kafin zaɓen 2023, lokacin da jam'iyyun adawa suka samu gagarumar nasara a jihar.

Bola: APC ta dura kan Atiku

An ji cewa jam’iyyar APC ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da barin burin siyasa ya rinjayi yadda yake mu’amala da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi maganar magudi da aka ba Yarabawa manyan mukamai a INEC

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben APC, Dele Alake, ya ce kiran shugaban kasar da “Bola” maimakon amfani da mukaminsa bai dace ba.

APC ta ce za ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ’yan Najeriya, nasarorin gwamnatin Tinubu da shirye-shiryen jam’iyyar yayin neman wa’adin mulki na biyu a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.