“Ka Ciyar Da Mutanen Kauyen”: Matashi Ya Kama Katon Kifi a Bidiyo, Ya Kinkimo Abunsa a kafada

“Ka Ciyar Da Mutanen Kauyen”: Matashi Ya Kama Katon Kifi a Bidiyo, Ya Kinkimo Abunsa a kafada

  • Wani mutum ya girgiza soshiyal midiya saboda wani katon kifi da ake tunanin ya kama
  • Ya zama abun kallo cikin mutane yayin da yake tare cike da karfin gwiwa da katon kifin ruwan a kafadunsa
  • Mutane da dama da suka kalli bidiyon suna ganin kifin zai yi daraja, wasu sun ce ya yi kama da shawo

Wani mutumi ya yi fice a soshiyal midiya bayan ya kama katon kifi a ruwa.

A wani bidiyon TikTok da ya samu mutum fiye da miliyan biyu da suka kalle shi, an gano mutumin wanda ya taki sa’a yana tafiya da katon kifin a kafadarsa.

Matashi dauke da katon kifi
“Ka Ciyar Da Mutanen Kauyen”: Matashi Ya Kama Katon Kifi a Bidiyo, Ya Kinkimo Abunsa a kafada Hoto: @lorenwyy
Asali: TikTok

Mutane na ta kallo da tsananin mamaki yayin da yake wuce su kamar soja a filin daga. Ya kai wani mataki sannan ya ajiye katon kifin a kasa.

Kara karanta wannan

Hadimin Gwamna da Aka Yi Garkuwa da Shi a Ramadan Ya Biya Kudi, Ya Fanshi ‘Yanci

Girma next kifin ya bai wa jama’a mamaki. Mutane na ta al’ajabin yadda ya kama shi, inda wasu ke ganin lallai zai kasance kifi mai tsada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@Kate Kwamboka ta ce:

“Wannan shine kifin da ya kifar da kawu Jonah.”

@sherriereal ta ce:

“Kifin nan ya kai kimanin shekaru 1000.”

Mya2004 ta ce:

"Ka ciyar da dukka kauyen kuma Za ka ga ya saura!”

@adinde_victor ya ce:

“Har sai ka gano kudinsa dala miliyan daya kuma ka yi farfesu da shi.”

Matashi ya kama kifi mai launin ruwan gwal a bidiyo

A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya ya garzaya shafin sada zumunta a don neman ba'asi bayan ya kama wani kifi mai launin ruwan gwal a cikin wani kogi.

Matashin dai ya ce bai sani ba ko kifi ne mai daraja kada ya je ya lamushe arzikinsa a cikin tukunya don haka ya bazama duniyar soshiyal midiya don samun karin bayani a wajen wadanda ke da ilimin sanin kifaye ko suka taba cin karo da irinsa.

Mutane da dama da suka ci karo da biyon nasa sun bayyana cewa wannan ba wani kifi ne na musamman ba domin dai ana samun shi a wasu yankunan kasar harma wata ta ce a yankin arewacin kasar ana yi wa kifin lakani da kurungu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel